Kasancewar jama'a da dama suna fama da wadannan matsalolin shi yasa muka zakulo muku wata fa'ida mai saukin hadawa domin ajarraba. Allah yasa adace:
ASAMU :
1. Garin Habbatus Sauda Cokali 7.
2. Garin tafarnuwa cokali 5.
Ahadasu acikin zuma kofi guda, agauraya a ajiye. Sannan marar lafiyan zai rika shan cokali 3 kullum da safe bayan ya karya. (after breakfast).
Zai ci gaba da yin haka har kwana 20. Sanan bayan nan asamu Man Habbatus Sauda irin na Misra ko Pakistan, kullum arika zuba cokali guda acikin ruwan shayi ana sha tare da zuma ko sikari. Safe da yamma.
Wannan maganin zai yi amfani sosai ga Masu fama da chutar Ulcer (Olsa) ko Rashin fitowar fitsari ko rikicin jinin haila. Ko matar da ruwan nononta ba ya zuwa sosai.
Kuma ana so mutum ya kiyaye aikata duk Abubuwan da zasu iya motsa masa rashin lafiyarsa ayayin da yake shan maganin nan.
Insha Allah za'a ga abin mamaki wajen samun waraka daga Allah (SWT) domin kuwa tushen wadannan magungunan yana nan acikin Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww).
Idan an jarraba an dace, tukwicinmu shine ayi ma Kasar nan addu'a Allah ya bamu zaman lafiya da kuma shugabanni Nagari.