Assalamu alaikum Malam da fatan alkhairi Allah ya kara lafiya da wadata. Allah kuma yasa muna cikin mabiya Shugaba wajen shiga aljannah saboda Annabi. Malam ga wasu tambayoyi da wasu suka rubuto Dan Malam in Allah yabada ikon amsawa ayi post saboda sauran 'yan uwa, shiyasa nace bari nace bari Na turo a amsasu a wannan Makaranta. Gasu kamar haka.
Ma'aikata ne Mu sai aka futo mana da tsarin Cooperative kuma ance idan mutum ya ranci kudi awajensu zai biya tare da interests kuma zasu sakawa duk wani members To Malam idan mutum bai ranci komai ba Iya kudinsa daya tara ya karba, ya wancen da suka Qara masa mutum zai cire ne yayi sadaka ko sun bata Dukiyar tasa gaba Daya.
2- Malam banki ne suka zo suke Neman customers ma'aikata idan ka fara tare da su salary mutum Na wata daya ya shiga account zasu bawa mutum rance kudi zasu cira a salary har shekara biyar, mutum ya Iya karba Dan gabatar da wani hidima NASA. Allah ya sakawa Malam.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Abisa fahimta ta Musulunci, dukkan wata huldar bashi ko ranche, ana yinta ne domin taimakawa juna. Amma duk wani bashi ko ranche wanda mutum zai rika biyan kudi fiye da abinda ya ranta, sunansa ya zama RIBA kenan. wato kudin ruwa. Shi kuwa kudin ruwa haramun ne.
Sai dai akwai abinda ake kira MUSHARAKA (cooperative banking) wanda mutane da yawa zasu iya hada kudadensu arika gudanar da wata harkar kasuwanci da kudin. Amma fa zasu rika raba faduwa (asara) kamar yadda zasu raba reebah. Wannan halal ne.
Shi wancan tsarin da kuke yi, wannan Qarin kudin ne ya saba ma addini. Amma da ace zaku rika gudanar da kasuwanci ne da kudin, sannan kuma duk wanda ya ranchi wani abu daga cikin kudin ba za'a dora masa kudin ruwa ba, to wannan ya halatta.
* Idan an baka kudin ruwa, Malamai sunce ba zaka ci ba. sai dai zaka iya bayarwa domin wasu su amfana dashi.
2. Mun riga mun fada tun farko. duk wani bashi ko ranche, mutukar dai akwai wani Qarin kudin da zaka biya sama da asalin abinda ka ranta, to wannan haramun ne.
WALLAHU A'ALAM.