An-naseer Muhammad Wrote:
Da farko idan zaka shiga dakin Amaryarka, zaka shiga ne da alwala.
Sannan zaka nemi 'Dan wani abinci mai daraja.
Misali kamar Naman Kaza, ko Tsire, da sauransu.
Idan Kashiga zaka umurceta itama taje tayi alwala.
Sannan kuyi Sallah raka'a biyu. Sannan kuyi ma Allah godiya abisa cika muku burinku da yayi. Kuyi addu'a abisa kanku da dukkan al'ummar da suka amsa gayyatarku suka halarci wajen daurin aurenku.
Daga nan sai ka dafa kanta. Ko goshinta, sannan ka karanta wannan addu'ar kamar haka:
"ALLAHUMMA INNEE AS'ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA 'ALAYYA.
WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIYYA
(ko kuma MA JUBILAT ALAIHA)"
(Abu dawud ya ruwaito da Ibnu Maajah da Nisa'I).
MA'ANA:
"YA ALLAH ina rokonka alkhairin da yake tare da ita, da kuma alkhairin abinda ka ginata akai. Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da kuma sharrin abinda ta ginu akansa"
Ita wannan sallar Nafilar da akeyi, tazo ne acikin ayyukan Sahabbai.
Kamar irinsu Ibnu Mas'ud (rta).
Daga nan kuma sai kuci wannan abin da ka shigo dashi, ku dan sha wani abu mai zaqi haka.
Amma ba'a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin.
Daga nan kuma sai ku kusanci juna, tare da gabatar da 'yan wasanni da juna kafin kufara gabatar da ibadar Aure.
Kuma akwai addu'ar da ake karantawa daidai lokacin da za'a fara jima'I ita ce:
"AllahuMMa Jannibnash Shaitan Wa jannibiSh-shaytana ma razaqtana"
MA'ANA: "Ya Allah ka nisantar da shaitan daga garemu.
Kuma ka nisantar da shaitan daga abinda zaka azurtamu dashi"
Annabi (saww) yace:
"Idan aka Qaddara samun ciki awannan saduwar, to shaitan ba zai iya chutar dashi ba har abada"
(Bukhary da Muslim suka ruwaito shi)
Kabi amaryarka ahankali.
Domin kuwa wasu amaren zaka iske sun wuni cikin gajiyar biki, sannan ga kunya ta lullubeta saboda tunanin wannan lokaci mai daraja..
Sannan yawancin angwaye suna kwallafa ransu akan cewar wai sai sunyi jima'I adaren farko.
Wannan ba dole bane.
Idan kaga alamar ta riga ta gaji, to ka kyaleta.
Idan kuma tsoro take ji, (musamman ma idan mai kananan shekaru ce, ko kuma Allah ya tsareta bata ta'ba kusantar namiji ba).
Zaka tarar ta gama tsorata, wata ma har tana karkarwa (jikinta yana rawa saboda tsoro).
Don haka ka kwantar mata da hankali ta hanyar kalamai masu dadi na soyayya, nasiha, da sauransu.
Haka shari'a ta koyar.
Allah ka aurar da matasanmu maza da mata ga Ma'aurata nagari.