Wani daga cikin magabata, wanda ma shiba musulmi bane.
Dayazo mutuwa yasa aka kira masa manyan sojojinsa sai yace musu, yanason su cikamar wasu wasiyoyi gudu uku, idan mai yanke kauna ta daukeshi.
Wasiyoyin kuwa sune kamar haka:
1. Likitocin da sukafi kowa kwareya a fadin kasarsa, su yakeso sudauki akwatin gawarsa sufito da'ita bainar jama'a kafin aje a binneshi.
2. Dukkan abin daya mallaka na kudi dana zinari ko azurfa, yanason a tattarasu a watsasu a hanyar daza'a bi da gawarsa zuwa makabarta.
3. Hannayensa kuma yace yanason a barsu a wajen akwatin suna Lilo inda kowa dake wajen zai iya gani.
Wani daga cikin sojojin nasa sai yayi mamakin wannan abun saiya tambayeshi karin bayani shi kuma sai yace:
1. Inason likitoci su dauki gawatane domin na nunawa mutane cewa yayinda mutuwa tazo ko da likitocin da sukafi kowa kwarewane, baza su iya warkadda mutum ba.
2. Inason a watsa dukiyata akan hanyane domin mutane susan cewa duk abinda aka samu a duniya, a duniya ake barinsa.
3. Inason abar hannayena suna rito ta wajene domin mutane su gane cewa munzo duniya hannu empty haka kuma zamu koma hannunmu empty babu komai, bayan dukkan abinda muka mallaka na dukiya da sauran kayayyakin duniya bayan mungama cinye dukkan kwanakinmu a duniya, kuma wannan shine lokaci.
Lokaci shine makiyinmu ba mutuwaba.
To masu karatu kunjifa kafiri ma kenan yanayi tunani irin wannan, balantana mu Musulmai, masuyin Sallah.
Ya Allah Kasa muyi amfani da lokutanmu wajen neman lahira bana duniya kadaiba.
Allah ka jiqanmu ka gafarta mana.