Azamanin magabata na kwarai akwai wani barawo wanda ya kware sosai wajen Shiga gonakin mutane yana satar Amfanin gona.
Yana da wani Qaramin yaro agida. Saboda haka kullum idan ya sayar da duk abinda ya sato, sai ya ajiye Tuffah (apple) guda daya ya tafi dashi gida ya kaima yaron nasa.
Rannan sai yaron yace "Baba ina so ka tafi dani ka kaini wajen da kake tsinkowa wannan Tuffah din".
Don haka sai baban nasa ya tafi dashi. Sai ya ajiye yaron daga wajen shingen sannan yace masa "Ka rika duba min. da zarar ka hango wani ya taho ka gaya mun don aganni acikin gonar nan".
Daga jin haka sai yaron ya fahimci cewa ashe Baban nan nasa BARAWO NE. don haka sai da ya bari baban nasa ya shiga cikin gonar yana ta yagan Tuffah sai yayi kiransa da karfi:
"BABA!! FITO DA SAURI GA WANI YANA KALLONKA!!".
Da uban ya fito aguje, ya leka kan hanya bai ga kowa ba, sai ya tambayi yaron "Kace ana gani na, kuma nq dubq banga kowa ba... Shin wanene mai kallon nawa?".
Sai yaron yace masa "ALLAH NE YAKE KALLONKA!!". Uban yana jin haka sai ya fashe da kuka.. ya kama hannun yaronsa suka koma gida. tun daga wannan ranar bai sake yin sata ba..
Ya tuba ya zama mutum mai tsoron Allah, mai tuna Allah ako yaushe... yana ganin tamkar agaban Allah yake yin komai.
Ya Allah ka sanya mana Taqwa acikin zukatanmu.