ABDULLAHI BN SALAAM shine shugaban Malaman Yahudawan Madeena. Yazo wajen Manzon Allah (saww) yace masa:
"Nazo ne domin inyi maka wasu tambayoyi guda uku. Babu wanda yasan amsarsu in ba Annabi bane.
1. Shin menene farkon sharadin Tashin Alkiyamah??
2. Shin menene farkon abincin da 'yan Aljannah zasu ci??
3. Mae yasa wani lokacin Yaro yakanyi kama da Mahaifinsa, wani lokacin kuma da mahaifiyarsa??"
Sai Manzon Allah (saww) yace masa "Yanzun nan Mala'ika Jibreelu yazo ya bani labarin amsoshin nan".
Sai yace "Mala'ika Jibreelu??"
Sai yace masa "Eh Mala'ika Jibreel". Sai yace "Ai wannan acikin Mala'iku shine Makiyin Yahudawa".
Sai Annabi (saww) ya karanto masa ayah ta 98 acikin suratul baqarah, sannan ya gaya masa amsoshin tambayoyinsa kamar haka:
1. Amma farkon sharadin tashin alkiyamah, wata wuta ce wacce zata koro mutane tun daga Mahudar rana har zuwa mafadarta".
2. Amma farkon abincin da 'yan Aljannah zasu ci, shine Hantar wani Kifi.
3. Idan maniyyin Namiji ya riga na mace sauka, to sai yaron yayi kama dashi. Kuma idan Maniyyin mace ya riga Sauka sai yaron yayi kama da ita".
Sai Abdullahi bn Salaam yace: "Na shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Hakika KAI MANZON ALLAH NE.
Hakika Yahudawa mutane ne masu Qage da sharri. Idan suka san cewa na Musulunta tun kafin ka tambayesu game dani, to zasuyi min Sharri".
Da sauran Yahudawan suka zo sai Manzon Allah (saww) ya tambayesu "SHIN MENENE MATSAYIN ABDULLAHI BN SALAAM ACIKINKU?".
Sai suka ce "Mafi alkhairin cikinmu ne, kuma 'dan gidan mafi alkhairin cikinmu. Sannan Shugabanmu ne, kuma 'Dan Shugabanmu ne".
Sai Manzon Allah (saww) yace : "SHIN YAYA KUKE GANI IDAN SHI YA MUSULUNTA?".
Sai suka ce "Allah ya tsareshi, ba zai musulunta ba!!".
Abdullahi bn Salaam yana jin haka sai ya fito daga inda yake 'boye, yace:
"ASH-HADU ANLAA ILAAHA ILLAL LAHU, WA ANNA MUHAMMADAN RASULULLAHI".
Daga jin haka sai yahudawan suka ce "Ai wannan shine mafi sharrin cikinmu, kuma 'dan gidan mafi sharrin cikinmu".
Sai Abdullahi bn Salaam yace "Ya Rasulallahi kaga abinda nake tsoro kenan tun farko (wato sharrin bakinsu)".
Sayyiduna Abdullahi bn Salaam (ra) ya Musulunta, kuma Musuluncinsa yayi kyau sosai. Har ma ya kasance 'daya daga cikin manyan Malamai acikin Sahabban Manzon Allah (saww).
Aduba Sahihul Bukhary hadisi na 4480.
ZAUREN FIQHU