Assalamu alaikum Jama'a.
Akwai wani Muhimmin al'amari wanda mutane da yawa suke ta turowa tambayoyi zuwa ga ZAUREN FIQHU akansa.
Wannan abu shine KAYAN MATA. Idan nace kayan mata ina nufin ire-iren wasu magunguna wadanda Matayen zamanin nan (Matan aure) suke amfani dasu domin neman jan hankali Mazajensu.
Yawancin Wadannan abubuwan ana kawosu ne daga Kasashen waje. Irin su India, China, Nepal, da sauran kasashen da suka shahara wajen Qirkirar abubuwan da suke da dangantaka da TSAFI.
Mafiya yawan Matayen Hausa/Kanuri/Fulani sunfi yarda da wadannan magungunan fiye da duk wata addu'a ko nafilfili da zaka ce suyi. Saboda zuciyarsu ta riga ta lalace.
Kuma magungunan Sun rabu zuwa gida Hudu kamar haka:
1. Akwai wanda za'a ce ma Mace ta shafa ajikinta ko afarjinta.
2. Akwai wanda za'a ce Mace ta turara Farjinta dashi kafin saduwa da maigidanta.
3. Akwai wanda za'a ce ma mace ta rika ci ko sha acikin abinci.
4. Akwai wanda za'a ce ma Mace ta sanya ma Mijinta acikin abincinsa, ko ta shafa masa ajikin Mazakutarsa yayin saduwa, ko ta sanya ajikin suturar da zai sanya.
To duk wadannan abubuwan zamu iya yi musu kudin goro muyi musu hukunci kamar haka:
1. Idan abun ya Qunshi halastattun abubuwan ci kamar su Kankana, ayah, da sauran tsirrai, kuma ba'a sanya wani abu na tsafi ko champi acikinsa ba, kuma ba'a gaurayashi da wani abu na Najasa ba, to wannan halal ne tunda kasancewarsa ya kunshi kayan abinci ne da tsirrai wadanda suke Qara ma jiki ni'ima.
2. Idan abun ya Qunshi wani abu na Najasa, kamar Maziyyin Mace, ko Jinin hailarta ko farcenta ko Gashin gabanta, ko naman wata dabba haramtacciya, ko jininta, to wannan Haramun ne Mutlakan. Bai halatta ita mace taci ba, kuma bai halatta ta shafa ajikinta, ko ta sanya ma Mijinta acikin abincinsa ba.
3. Idan maganin ya Qunshi wasu turarurruka ko saiwoyi wadanda aka tsafasu ta hanyar sihiri domin gusar da hankalin Namiji, ko karkatar da zuciyarsa daga wani wajen zuwa wani wajen, to hakika shima wannan HARAMUN NE mutlakan.
Hakanan duk abinda suke bayarwa domin Mallakar Hankalin Namiji, ko Mallakar dukiyarsa, to wannan shima haramun ne.
Mafiya yawan wadannan abubuwan duk bokaye ne suke Qirkirarsu, sannan su bama dillalansu suzo suna saidawa.
Ya Ku Mata!!! Kuji tsoron Allah, ku guji neman hallaka kanku ta hanyar bin son zuciya da neman abin duniya.
Halastacciyar hanyar Mallakar Miji ita ce ladabi, biyayya da girmamawa.
Akwai wasu Mata wadanda suke kamar manyan dillalan wadannan magungunan. Har suna da groups a facebook da whatsapp domin tallatar da hajarsu.
Kwanakinn baya naga wani cin mutuncin da suka yima wasu bayin Allah saboda sunce bai halatta ayi amfani da maganinsu ba. Sunce wai hassada ake musu, wai saboda anga maganinsu yana karbuwa!!
Ni ashirye nake da duk wani CIN MUTUNCIN da zakuyi min. Gaskiya ce na riga na fadeta. Ban sanku ba, baku sanni ba, ballantana inyi muku kyashi ko Hassada. Bukata ta ita ce in tsamo zuciyoyin mutanen da kuke kokarin dulmiyarwa.
Bissalam.
Daga Zauren Fiqhu.