{1}. HASSADA:
Hakika Hassada tana daya daga cikin abinda yake cutar da al'umma.
Manzon Allah (S.A.W) Yace:
"Kashedin ku da hassada domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye Auduga.
{2}. ANNAMIMANCI:
Annamimanci shima yana cutar da al'umma.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
"Lokacin da aka yi mi'iraji dani mun wuce wasu mutane masu zara-zaran kumba, (farce) suna jan naman fuskokinsu, da jikkunan su, sai nace su wanene wadannan Ya Jibrilu ???
Sai yace sune wainda suke cin naman mutane.
Don haka akwai tanadin azaba mai tsanani ga masu cin naman mutane.
{3}.GIRMAN KAI:
Kowa da irin nasa nau'in girman kan.
Akwai girman kai na rashin karban gaskiya.
Akwai kuma girman kai na wulakanta Jama'a.
Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Mai girman kai koda kwayen zarrane bazai shiga Aljannah ba.
4.GIBA:
An tambayi Manzon Allah (S.A.W) menene Giba ???
Sai yace ka ambatawa dan'uwanka abinda baya so.
5.KARYA:
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
"Yana daga cikin manyan laifuka kabawa dan'uwan ka labari, shi yana dauka gaskiyane amma kuma kai karya kakeyi, wannan shima yana cutar da al'umma, domin karya tana leading mutum zuwa ga Abubuwa masu yawa, kada kaji tsoro ko faduwar gaba indai abinda kake fada gaskiyane, koda dukkan mutane zasu ki yarda dakai.
6.KADE KADE DA RAYE RAYE:
Tabbasa yawan jin waka yana kashe zuciyar bil Adama yana lalata zuciya, yana kuma haifar da sharri, yana kuma samar da mummunar dabi'a.
Wani sai yayi sati bai karanta Qur'aniba, kuma baya saurara, wanima gani yake kauyancine saka karatun Qur'ani acikin wayarsa, domin su zigi zasuce bai
wayeba.
Zaka sami mutum yana da Memory Card mai nauyi, amma ba abinda yake ciki sai wakoki da videos masu nauyi, hakika dan'uwa ko 'yar uwa duk wadanda suke aikata haka to sun dauko hanyar halaka.
ALLAH KA KAREMU DAGA WADANNAN MUNANAN AYYUKAN.