Malamai sunce dangane da imani, Allah ya raba halittunsa masu hankali ne zuwa gida uku kamar haka:
1. Akwai wadanda Allah ya haliccesu da imaninsu kuma imanin nasu kullum Qaruwa yakeyi acikin kowacce kiftawar ido suna Qara zurfi cikin Imaninsu. Wadannan sune Annabawa da Manzanni (alaihimus salam).
2. Akwai wadanda tunda Allah ya haliccesu, yayisu ne da cikakken Imaninsu. kuma imanin yana nan bisa yadda aka haliccesu tun farko. ba ya Qaruwa kuma ba ya raguwa. wadannan sune Mala'iku.
3. Akwai kuma wadanda Allah ya haliccesu da imani azukatansu. Sai dai ya sanya musu mantuwa. Saboda haka suna bukatuwa zuwa ga wanda kullum zai rika tunasar dasu domin gyaruwa da habbakuwar imaninsu.
Su imaninsu yana raguwa kuma yana Qaruwa gwargwadon yadda suka tsinci kansu acikin biyayyar Allah ko sa'bonsa. Wadannan sune nauyayan nan guda biyu. wato MUTANE DA ALJANU.
Mutane da Aljanu su kadai ne suke iya sa'ba ma ALLAH. sune wadanda ake samun kafirai da munafukai acikinsu.. shi yasa Allah cikin Rahamarsa da tausayinsa garemu ya turo mana da Manzanni daga gareshi, suka zo cikin siffarmu suka rayu acikinmu.. Suna da siffar halitta irin tamu amma ba kamar tamu ba..
Ya basu aikin isar ma halittu sakon Ubangijinsu. Suka zama masu gargadi da kuma bishara. wanda ya bisu yayi imani dasu, ya aikata umurnin da suka zo dashi, ya hanu daga abinda suke gargadi akansa, to ya zama mumini.
wanda kuwa ya karkace yaki yin imani dasu to ya zama KAFIRI. Wanda kuma yayi imani dasu afili, amma zuciyarsa bata karbi Imanin ba ya zam Munafuki.
Wanda kuma yayi Imani dasu har Zuciyarsa amma duk da haka wani lokacin shaitan yakan rinjayeshi har ya aikata abinda Allah ya hanashi, to wannan bai fiddashi daga imani ba.. Sai dai Imanin nasa ne yake raguwa yana yin Qasa..
'Yan uwa muyi recharging din imaninmu ako yaushe da yawan zikirin Allah safe da yamma da Karatun Alqur'ani mai girma..
Allah shi kare mana dukkan Imaninmu.
ZAUREN FIQHU.