Assalamu alaikum Malam. Shin ya halatta Mace Tay ma Mijinta Sadaka bayan rasuwarsa? Na tambayi wasu mutane suka ce wai Haram ne. Shin yaya abun yake.
(daga wata baiwar Allah)
AMSA
======
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
A'a yin sadaka domin Mamaci, abu ne mai kyau. Ba haram bane. Ba kuma bidi'a bane.
Yana zamantowa Haram ne idan anyi amfani da dukiyar magada wajen yin Sadakar. Amma idan kikayi amfani da kudinki naki na kanki, to wannan babu komai. ya halatta.
Sannan kuma yakan zamanto bidi'a ne idan har aka Qayyade wasu kwanaki na musamman domin yin sadakar. Misali kamar Sadakar Uku, sadakar bakwai, ko Sadakar cikar shekarar mamaci. Wannan duk bidi'o'i ne.
Amma zaki iya yi masa sadakah duk lokacin da kika ga dama, Kuma zaki iya yi masa duk wani aikin Alkhairi na nafilfili irin su Umrah ko gina Makaranta, ko Masallaci ko Rijiya duk dominsa. Allah zai bashi ladan.
Da fatan Allah ya jikan dukkan al'ummar Musulman da suka rigamu tafiya. Mu kuma Allah yasa mu cika da kyau da Imani.
WALLAHU A'ALAM.