TAMBAYA TA 1556
*******************
Assalamu alaikum malam tambayace daga wata baiwar Allah take cewa:- Munravu Da Mijina, Kuma Nina Kasance mace ce Mai Yawan Bukata Gashi Vana Iya Axumi, Ina Yawan Kallan Hotuna Na Batsa Haka Dan Ragewa, Amma Banasamun Nutsuwa, Ko Da Shawarar Da Xa,a Bani Kan Hakan?
Assalamu alaikum malam macece a duk lokacin da su sadu da mijinta nonon ta kawai yake sha kuma gashi tana da karamar jinjira wai har ya kan shanye ruwan nonon duka yarinyar bata samun nasha idan har tafiya zai yi yakan so ta tatsi nonon ta bashi ya tafi da shi to wai dan Allah ya wannan alamarin ya ke a musulunci meye kuma matsayin wannan dan Allah ina jiran mafita.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Kallon hotunan batsa haramun ne. babu wani dalilin da zai sa ya zama halal gareki wai don ke kina da Tsananin bukatar Jima'i.
Allah yana cewa:
"KUMA KACE MA MUMINAI MATA SU RINTSE IDANUWANSU (DAGA KALLON DUKKAN ABINDA BAI HALATTA GARESU BA) KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU (DAGA ZINA, MADIGO, DA SAURANSU). KUMA KAR SU RIKA BAYYANAR DA ADONSU SAI DAI ABINDA YA FITO FILI DAGA CIKINTA".
Kin ga acikin wannan ayar Allah ya haramta miki duk irin wadannan miyagun kallace-kallacen. domin yin hakan zai iya kaiki zuwa ga aikata zina. (Allah shi kiyayemu).
Maimakon haka gara kije ki nemi daidaitawa da mijinki, ya mayar dake amatsayin matarsa. idan kuma hakan bata samu ba, kiyi fatan Allah ya fito miki da wani miji nagari.
2. Miji ya tsotsi nonon matarsa yayin da suke gabatar da sunnah wannan addini bai haramta ba. Sai dai kuma bai kamata shi mijin nata ya mayar da nonon tamkar abincinsa ba.
Wannan yazo da bakon abu wanda zai iya zama chutuwa agareshi ko ga ita matar tasa ko kuma yarinyar da take shayarwa.
Don haka ya kamata yaji tsoron Allah ya dena ketare iyaka. Mutum ya tsaya inda addininsa ya tsaida shi, kuma ya kyautata Dukkan mu'amalarsa ta auratayya.
Shan nono wanda yaje haramta aure shine wanda aka yishi alokacin da mutum yake yaro karami bai isa yaye ba. Kuma sai ansha kamar sai biyar (cikakkun sha tare da koshi).
WALLAHU A'ALAM.