Muhammad ibnu Suhnoon (ra) yace dukkanin malamai sun hadu waje guda akan cewar Duk wanda ya zagi Manzon Allah (saww) ko kuma ya fadi wata magana wacce ta tauye darajarsa, to KAFIRI NE. Akwai azabar Allah mafi radadi akansa.
Hukuncinsa kuma awajen al'ummah shine KISA. kuma duk wanda yake Kokwanto akan kafircinsa shima ya kafirta.
Tatacciyar magana daga malamai ita ce : Duk wanda ya zagi Manzon Allah (saww) idan shi musulmi ne to ya kafirta kuma kasheshi za'ayi. ba tare da wani sabani ba. wannan shine hukuncinsa bisa fahimtar dukkan Malaman Mazhabobin nan guda hudu, harma da sauran malamai.
Is'haq ibnu Rahawaihi ya ruwaito ijma'in Malaman Musulunci akan wannan mas'alar.
Kuma sunce idan mutumin da yayi zagin ba musulmi bane, amma yana zaune ne acikin Qasar Musulmai, to hukuncinsa dai shine KISA. bisa fahimtar Mazhabin Imamu Malik da kuma sauran Malaman Madinah.
Kuma wannan Hakanan shine hukuncin abisa fahimtar Mazhabin Imamu Ahmad da Mazhabin Malaman Fiqhun Hadisi. Imamu Ahmad ya fadi wannan sosai acikin rubuce rubucensa.
Abdullahi bn Ahmad yace : Naji Imamu Ahmad yace duk wanda ya zagi Manzon Allah (saww) ko kuma ya fadi wata maganar da zata tauye darajojinsa to hukuncinsa shine KISA. ko musulmi ne ko kafiri.
Aduba cikin :
ASH-SHIFA' ta Alqadhy Iyaadh : Shafi na 134.
SARIMUL MASLOOL na Ibnu Taimiyyah shafi na 4.
Daga ZAUREN FIQHU :