TAMBAYA TA 1555
********************
Assalamu Alaikum,
Allah ya taimaki Mallam, ya kuma kareka daga sharrin makiya, da kuma dukkan musulmai baki daya. Mallam tambaya nake dashi kamar haka: Nine nake aiki a ma'aikatar gwamnati, a karkashin wata hukuma da take shirya jarrabawa a ma'aikatan gwamnati, to a tsarin ni ina karkashin 'Director' ne, to kuma akwai 'Staff Officer wanda shine alhakin al'amuran jindadi da walwalar ma'aikata yake hannunsa, sai kuma mataimakinsa shine wanda yake da alhakin duk wani lamari na ma'aikata a wannan ofis namu, saboda iya aikinsa ya zamana duk aikin Staff Officer din shine yake yi (an danka masa komai a hannunsa), amma shi mutum ne wanda yake da son zuciya da kuma almundahana. A halin da ake ciki yanzu ya sameni akan wani mutum yayi jarrabawa kuma baici ba, akan lallai sai na gyara masa, rashin bashi hadin kai daga gurina zai iya kawo mun cikas a cikin aikina, kuma ya karbi kudi a gurin wannan mutumin masu tarin yawa da sunan zai taimake shi, to ni saboda kar ya bata mun al'amarina nayi masa abinda yake so, sai ya bini har gida ya kaimun kudi (wani abu daga cikin abin da wancan mutumun ya bashi). Na karbi kudi saboda amma banyi amfani da su ba, saboda tsoron kaucewa shubuha, shin mallam wacce irin nasiha zaka mun ni da yan'uwa musulmai akan yadda zamu gyara aikin mu, kuma shin wadannan kudin da ya bani nayi sadaka dasu gaba daya banyi amfani dasu ba, kuma ba don na samu lada ba, na niyyar na kauce ma wannan abin, shin yaya matsayin wannan abin yake.
Nagode, Allah ya saka da alheri. A boye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika karbar cin hanci domin taimaka ma wani mutum ya samu matsayin da ya wuce kokarinsa, abu ne wanda yake haramun. Allah ya hana.
Manzo (saww) yace : "ALLAH YA TSINE MA WANDA YA BAYAR DA CIN HANCI DA KUMA WANDA YA KARBA".
- Ibnu Maajah hadisi na 2,313.
Don haka wannan abinda abokin aikinka ya aikata ba Qaramin laifi bane. Muna fatan Allah ya shiryeshi.
Kai kuma in dai da gaske ne cewa ka bashi hadin kai ne don gudun sharrinsa, kar wani mummunan abun ya sameka, to kaga gaba dayan laifin ya sake komawa kan wannan Ubangidan naka.
Ta dalilin wannan abin da ya faru, Allah ne kadai ya san yawan adadin mutanen da zasu chutu bisa wannan takardar da kuka bama mutumin da kokarinsa bai kai ba.
Wannan nadamar da kayi, da kuma sadakar key din da kayi, duk alamomi ne wadanda suke nuna cewa ka riga ka tuba.
Din haka kaje kaci gaba da yin Istigfari da ibadu masu kyau da sauran zikirori. insha Allahu zaka samu karbuwar tuba daga Allah.
Ina jan hankalin 'yan uwa Musulmai masu aikin gwamnati da masu aikin kampanoni cewa muji tsoron Allah mu nisanci duk abinda zai janyo mana tsinuwar Allah data bayinsa.
Cin hanci bala'i ne. Allah ya rabamu dashi.
WALLAHU A'ALAM.