Assalamu alaikum, Allah shi gafarta Malam menene hukuncin yin Kiss tsakanin Namiji da dan uwansa Namiji? ko kuma tsakanin Mata Qawayen juna?
Don naga wasu Students suna yine. suna RUNGUMAR juna, kuma suna yin Kiss abakinsu. Don Allah ataimaka mana da amsar wannan tambayar domin zata Zama dalilin shiryuwar wadansu Insha Allah.
Daga Almajirinka, Muhammad Isa
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Gaskiya yin irin wadannan abubuwan kwata-kwata ya kauce ma Shari'ar Allah. Bai halatta mutane su rika aikata duk wani abinda zai iya kaisu ga aikata manyan laifuka ba.
Anas bn Malik (ra) yace wani Mutum ya tambayi Manzon Allah (saww) "Ya Rasulallahi shin idan mutum ya hadu da 'Dan uwansa ko abokinsa zai kwanta masa ne?"
Sai yace "A'A" sai Mutumin yace "To zai rungumeshi ya Sumbaceshi ne?" Sai Manzon Allah (saww) ya sake cewa "A'A".
Sai Mutumin yace "To shin zai rike hannunsa yayi musafaha dashi ne?" Sai Manzo (saww) yace "EH".
– Hadisi na 2,728 acikin Sunanut Tirmiziy.
Dukkaninmu Mun san cewa Musulunci ya kan haramta duk wani abinda zai iya kaiwa zuwa ga aikata miyagun laifuka. Shi yasa ma aka haramta kadaituwa tsakanin Mace da duk wani namiji wanda ba muharraminta ba. Kuma ya haramta Mace tayi tafiya ita kadai ba tare da miji ko Muharraminta ba. Kuma Musulunci ya haramta Kallon Matar da ba taka ba, ko Mijin da ba naki ba.
Musulunci ya hana kadaituwa da 'Yan Daudu ko kuma irin samarin nan Shagirai (Wadanda suke kama da mata saboda Fuskokinsu babu gashi.
Kuma Musulunci ya haramta Maza guda biyu su kwanta bisa shimfida guda, cikin mayafi guda. kamar yadda ya haramta ma Mata ma yin hakan atsakanin junansu.
To kaga duk wadannan an haramtasu ne saboda zasu iya kai mutum zuwa ga aikata Zina ko Luwadi ko Madigo.
Manzon Allah (saww) yace "KAR WANI NAMIJI YA KALLI AL'AURAR WANI NAMIJIN, KUMA KAR WATA MACE TA KALLI AL'AURAR WATA.
KUMA KAR MAZAJE BIYU SU KWANTA KARKASHIN MAYAFI GUDA, KUMA KAR WATA MACE TA KWANTA KARKASHIN MAYAFI GUDA TARE DA WATA MACEN"
Bai halatta Namiji ya rungumi dan uwansa namiji, ko mace ta rungumi 'yar uwarta mace ba, ballantana har arika sumbartar juna.
Sai dai idan wani daga cikinsu ya dawo ne daga wata tafiya, an dade ba'a hadu ba, to Hadisi ya nuna halarcin rungumar juna. amma banda yin Kiss.
Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "SAHABBAN ANNABI (SAWW) SUN KASANCE IDAN SUN HADU SUNA YIN MUSAFAHA NE. AMMA SUKAN RUNGUMI JUNA IDAN 'DAYANSU YA DAWO NE DAGA TAFIYA"
- Tabaraniy da Baihaqiy ne suka ruwaitoshi).
Jabir bn Abdillah Al-Ansariy (ra) yace yayi tafiyar tsawon wata guda zuwa Sham wajen Sayyiduna Abdullahi bn Unays (ra) da ya fito ya ganshi sai ya rungumeshi, shima ya rungumeshi.
– Imamul Bukhariy ya ruwaito acikin ADABUL MUFRAD da Imamu Ahmad acikin Musnad juzu'i na 3 shafi na 495.
To amma duk da haka kaga ba'a ce suna yin Kiss da junansu ba. Don haka irin abin nan da kace samari ko 'yan mata Students suna yi yau da kullum kwata-kwata bai halatta ba.
Wallahu a'alam.
Source Zauren Fiqhu