Assalamu alaikum malan barkanmu da wannan ranar mai girma Allah ya bamu
ladan sallarmu..
Malam dan Allah, yaya sanya zobe ko sarka suke ga da
namiji cikin addinin musulunci? Shin haramun ne? sannan kuma malan shin ko krista
idan yana aikin kwarai, shin yana da rabo ga aljanna koda bayya salah?
Allah yasa mu dace..
- Daga Muhammadou Toukour
AMSA
*****
Wa alaikumus Salam wa rahmatullah.
Hakika Sarka da 'Dan-kunne da warwaro, wadannan duk kayan ado ne na Mata. Haramun ne Namiji ya sanyasu. Bisa Hujjah ta hadisin da Abdullahi bn 'Abbas (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) wanda yace:
"Manzon Allah (saww) ya tsine ma Maza masu kamanceceniya da Mata, da kuma Mata masu kamanceceniya da Maza".
- Sahihul Bukhary hadisi na 5,435.
Acikin hadisi na 5,436 na Sahihul Bukhary Manzon Allah (saww) ya Qara tsine ma duk Mazan da suke kokarin koyi da Mata, da kuma Mata masu yin koyi da Maza, Kuma yace KU KORESU DAGA GIDAJENKU".
Al-Imam Mubarakpooriy (rah) ya fada acikin TUHFATUL AHWAZIY cewa:
"Maza masu yin kamanceceniya da Mata, sune wadanda suke yin koyi dasu ta wajen Muryarsu, da suturarsu, da kayan adonsu, da maganarsu, da tafiyarsu".
Don haka sanya sarka ko dan-kunne HARAMUN ne ga Namiji Musulmi.
Acikin irin wadannan kayan adon, ZOBE ne kadai ya halalta. Domin an ruwaito cewa Manzon Allah (saww) yana da Zobe na Azurfa (Silver) don haka ya halatta ga Maza su sanya zobe.
2. Duk abinda kafiri zai aikata na alkhairi ba zai samu wani lada ba koda Qankani. Domin kuwa Allah yana cewa:
"Misalin wadannan da suka kafirta, ayyukansu kamar misalin Kawalwainiya ne acikin rairayi, Mai jin Qishirwa yana tsammani ko ruwa ne, har sai yaje wajensa sai ya tarar cewa ba komai bane. Kuma zai tarar da Allah awajensa zai cika masa hisabinsa, Allah mai gaggawar sakamako ne".
(Suratun Nour, ayah ta 39).
Imani yana daga cikin sharadin karbuwar aiki. Kuma shi kafiri bashi dashi.
Wallahu a'alam.