TAMBAYA TA 1531
***************
Assalamu alaikum. Allah shi gafarta Malam, Menene hukuncin matar da take da alwala amma ta wanke ma yaronta kashi, ko kuma ta ta'ba wandonsa wanda yake Qunshe da kashi?
Shin alwalarta tana nan ko ta karye?
2. Menene hukuncin Matar da take cikin sallah kuma sai yaronta yayi mata fitsari?
3. Shin menene hukuncin alwalar Namiji ko Mace idan suka ta'ba al'aurar yaro Qarami, ko Qaramar yarinya? Shin alwalarsu tana nan ko kuma ta karye?
Allah shi Qara ma Malam lafiya cikakkiya tare da imani ya kuma Qara maka Son Manzon Allah (saw).
(Daga Ahmad Abdalawy Kila).
AMSA
*****
Wa alaikumus Salam wa Rahmatullah.
Matar da take da alwala, kuma sai yaronta yayi mata fitsari, ko kuma ta taka fitsari ko kashi, ko kuma ta ta'ba, to alwalarta tana nan. Babu abinda ya samu alwalarta.
Hukuncinta shine: Ta wanke hannunta wanda ta ta'ba najasar dashi. Idan kuma takawa tayi, to taje ta wanke Qafarta amma alwalarta tana nan.
Hakanan wacce yaronta yayi mata fitsari alhali tana cikin sallah, to sallarta ta 'baci. Zata je ta cire suturar da fitsarin ya ta'ba, sannan ta wanke jikinta tazo ta sake sallarta.
3. Ta'ba al'aurar Qananan yara ba ya karya alwala. Mutukar dai ba'ayi hakan don sha'awa ba. Don haka matar da tayi ma yaronta wanka ko kuma ta shafi al'aurarsa yayin wanke masa fitsari ko kashi, alwalarta tana nan.
Sai dai ana so ta wanke hannunta sosai saboda yiyuwar ko najasa ta makale ajikin hannunta.
Wallahu a'alam.
source ZAUREN FIQHU