Assalamu alaikum malam mungode Allah ya saka da Alheri da irin gudunmuwa da kake bawa al umma tambaya anan shine aure ya halatta tsakanin Namijin da yake shafa budurwarsa kullum yaje fira zai rungumeta ta.rungumeshi ya shafa mata nononta yayi mata kiss a bakinta? Dan Allah zai iya aurenta? aure ya halatta a tsakaninsu?
(daga wata baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Aure bai haramta tsakaninsu ba, mutukar dai basu taba yin zina (saduwa irin ta jima'i) da juna. Da ace sunyi ainihin zinar ne, to aure zai haramta atsakaninsu har sai sunyi cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake karba.
Hakika duk wadanda shaitan ya rudesu suka aikata irin wannan fasadin na Tattaba juna, ko rungumar juna, sun riga sun cire duk wata albarkar auren nasu tun daga nan.
Allah (SWT) yana cewa:
"KADA KU KUSANCI ZINA. DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYA CE MUMMUNA".
Manzon Allah (saww) yana cewa:
"WALLAHI A SOKI 'DAYANKU DA KIBIYAR BAQIN QARFE AKAYINSA, YAFI ALKHAIRI GARESHI DA ACE YA SHAFI JIKIN MATAR DA BATA HALATTA GARESHI BA".
Ya zama wajibi kuji tsoron gamuwarku da Allah. ku rika tuna ranar fitan ranku.. kwanciyar kabarinku, tsayuwarku agaban Allah, awun hisabi, haye siradi, da dai sauran al'amura Manya wadanda suke gaban kowanne mutum musulmi ko kafiri.
Ya Allah ka kiyayemu daga kowacce irin ALFASHA don alfarmar Annabin da ka saukar ma Alqur'aninka.
WALLAHU A'ALAM.