Blue films fina finai ne da wasu tsageru daga cikin yahudawa suke shiryawa wanda yanada illa sosai.
Domin yanzu anyi ittifakin cewa ba abinda yake saurin rufta mutum zuwa zinace-zinace kamar shi kallon blue film din wanda zamani yazo dashi baga namiji ba ba kuma ga mace ba.
Babban abin takaici yanzu yan mata sunfi kowa kwarewa wajan
iya kallon wannan lalaci na blue film.
Hukuncinsa:
Kallon tsaraici haramun ne a shari'ar musulunci in banda na matarka ko Namijinki ballan tana
kuma kallon saduwa tsakanin Mazinata wannan abune mai matukar muni sosai.
Allah yana cewa:
"Ka gayawa muminai maza su rintse ida Nuwansu daga kallon haram kuma su kiyaye farjinsu daga yin zina.
Yan uwa mu kiyaye duk wanda yake kallon irin wandannan abubuwa to lalle yayiwa Allah tawaye.
A wani gurin Allah yana
cewa:-
Kada ku kusanci zina hakika ita zina Alfasha ne kuma mummunan
hanyace.
Kunga saboda halakar da take cikin zina sai Allah yace kada mu
kusan ceta shi kuwa irin wannan
kallon yakan sanya masu yinsa su afka cikin zina kai tsaye.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"Allah ya tsinewa mai kallon tsaraici da kuma wanda ake kallon tsaraicin nasa.
Daga karshe ina Qara jawo hankalin masuyi sutuba su daina.......!!!
YA ALLAH KA TSARKAKE MANA ZUKATANMU