Ga hanyoyin nan zan bayyanasu kamar yadda nayi muku alkawari. Kuma na tabbata zakuyi mamakin wasu daga ciki. Amma na tattaro ne daga Sahihan labarai da suka iskeni, da kuma abinda na karanta cikin litattafan maluma :
1. Akwai wacce boka zai sanyata ta aske gashin gabanta da gashin hammatarta sannan ta tsakuro gashin kanta da Qumbarta. Zata kaima bokan shi kuma ya Qonasu ya chakuda cikin maganin. Sannan ya bata ta rika sanya ma mijinta cikin abincinsa. (Bayan shirkar ma Qazanta ce Qarara).
2. Akwai wacce bokan zai ce ta tube tsirara, ya aske mata gabanta, sannan ya rubuta mata sunayen wasu Manyan Aljanu. To da zarar mijinta ya sadu da ita shikenan wadannan aljanun ne zasu shiga jikinsa su karkatar da zuciyarsa daga kan KOWA sai ita!!
3. Akwai wacce bokan zai rubuta sunayen shaitanun Aljanun tare da ayoyin Alqur'ani sannan ya bata taje tayi Tsarki dashi, ta rika bama Mijin nata acikin ruwan shansa!!
4. Akwai wacce bokan zai nannade bakin zare ko wani abu na tsafi ajikin al'aurarsa, yayi Zina da ita, sannan ya dauko abin ya hada mata magani dashi.... Subhanallah.
5. Akwai wacce bokan zai bata maganin yace ta debi ruwan Maniyyinta, ko ruwan Wankan gawa, sannan ta rika bama Mijinta acikin abincinsa.
6. Akwai wacce bokan zai sanya ta kawo masa Tsumman da tayi Qunzugun jinin haila dashi, Bokan zaiyi rubutu ajiki sannan ya bata ta binne awani waje inda mijin nata zai tsallaka. (Wannan yana daga cikin cases din sihiri da aka ta'ba kawo mana anan. Kuma mutumin ya samu lafiya sosai ya warke daga baya. Falillahil Hamdu).
7. Akwai wacce bokan zai bata wani magani, su hada da Zuciyar kare, ko Alhanzir, ko dai wani Qazamin abu sannan ta barbada ma Mijinta a abinci. (Wallahi wannan Aljanun sihirin sun kusan haukatar dashi ma. Domin ko unguwa zata je sai ya bita, kuma idan ran matarsa ya baci, sai ya fashe da kuka yana bata hakuri kamar yaro karami).
8. Akwai wacce Bokan ya bata wata tsokar nama ta Tsafi, ta sanya cikin farjinta yayin da take haila. Bayan ya gama ta kawo masa, suka hada da kulumbotonsu sannan taje ta barbada a abincin Mijinta. (Wallahi wannan akan idonmu abin ya faru. An kawo mana Case din, Allah ya tona asirin Matar har da Uwarta wacce ta karbo mata maganin, munyi musu nasiha sannan muka sallamesu).
Wallahi ire-iren wadannan Cases din suna da mutukar yawan da ba zamu iya lissafosu gaba daya ba. Sai dai muce Allah ya shiryar da masu yi, mu kuma Allah shi kiyayemu daga sharrin bokaye da matsafa Mata da Maza.
Source... ZAUREN FIQHU