Allah ya riga ya tsine ma Iblees (shaitan). Shi kuma shaitan yayi rantsuwa agaban Allah cewa sai ya dulmiyar da mafiya yawan 'Ya'yan Adamu (as) tunda akansa aka Tsine masa.
Don haka shaitan yayi kokari ya samu wakilai daga cikin 'Ya'yan Adamu wadanda ya ajuyesu musamman domin su rika tayashi aikin hallakar da duk wanda suke da iko akansa.
Wadannan wakilai na shaitan sun hada da BOKAYE, MATSAFA, 'YAN-BORI, 'YAN TSUBBU, da sauransu.
Su kuma Mata saboda Kasancewarsu masu raunin zuciya da Qarancin zurfafa tunani akan al'amura, shi yasa suka zama sune manyan dillalai ga wadannan wakilan na shaitan. Shaitan ya mamaye zuciyarsu ya chusa musu tsananin son duniya da Qarancin tunanin lahirarsu.
Suna ziyartar wadannan wakilan shaitan din domin neman samun biyan bukatarsu ta duniya bisa kowacce hanya. komai muninta.
Na san da yawa daga cikin Daliban ZAUREN FIQHU zasu yi tunanin ko zan bayyana hanyar da bokayen suke bi domin hada magungunan. A'a ba zanyi haka ba. sai dai zan bayyana kadan daga cikin alamomin da zaki gane cewa abu kaza shirka ne, Koda an baki kinga ba zakiyi amfani dashi ba, kuma ba zaki sake ziyartar duk wanda yake hulda da irin wadannan abubuwan ba.
Sai a post dinmu na gaba zan rubuto wasu daga ciki.
source...ZAUREN FIQHU