BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salati da aminci su tabbata bisa fiyayyen halittu, Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da tsarkakan iyalan gidansa masu albarka, da yardaddun Sahabbansa masu kwazo da dukkan mabiyansa har zuwa ranar Alkiyama.
Har yanzu dai muna magana ne akan hakurinsa (saww).
5. HAKURINSA BISA JINYA KO RASHIN LAFIYA IDAN TA SAMESHI (SAWW).
* Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (Allah shi yarda dashi) yace:
"Na shiga wajen Annabi (saww) alhali shi yana ciwon ciki. Sai nace masa: "Ya Rasulallahi ashe kana ciwon ciki haka mai tsanani?"
Sai yace "KWARAI KUWA. NI INA YIN CIWON CIKI KAMAR IRIN YADDA MUTUM BIYU DAGA CIKINKU SUKEYI (WATO ANA NINKA MASA CUWON KENAN)".
Sai nace "Hakane, wato kana da ninkin lada biyu kenan?"
Sai yace "EH WANNAN HAKANE. BABU WANI MUSULMIN DA WATA CUTARWA ZATA SAMESHI, GWARGWADON SOKEWAR QAYA, KO SAMA DA HAKA FACHE SAI ALLAH YA KANKARE MASA KURAKURENSA SABODA ITA, KUMA YA SHAFE MASA ZUNUBBANSA KAMAR YADDA BISHIYA TAKE ZUBARWA DA GANYENTA".
Imamul Bukhary ya ruwaito hadisin akan lamba ta 5,667.
Imamu Muslim ma ya ruwaito akan lambar hadisi na 2,571.
* Hadisi na biyu daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudry (Allah shi yarda dashi) ya shiga wajen Manzon Allah (saww) sai ya ganshi yana cikin Zazzabi har an sanya tsumma an daure masa kansa dashi.
Sai ya sanya hannunsa asaman tsumman da aka daure kan dashi.. (yaji yanayin zafin zazzabin) sai yace:
"Mamakin zafin zazzabin nan naka Ya Rasulallahi!"
Sai yace "MU (ANNABAWAN ALLAH) HAKA AKE TSANANTA MANA BALA'I, KUMA ANA NINNINKA MANA LADA".
- Aduba Sunanu Ibni Maajah, hadisi na 4,024.
- MUSTADRAK na Imamul Hakim, juzu'i na hudu shafi na 307.
* Hadisi na uku daga Sayyiduna Huzaifah ibnul Yamaan shi kuma ya karbo daga Goggonsa ('yar uwar mahaifinsa) Fatima (Allah shi yarda dasu) tace:
"Munje wajen Manzon Allah (saww) tare da wasu mata domin mu duboshi alhali yana cikin zazzabi, sai yasa aka dauko wata jakar ruwa (kamar gora, amma ta fata).
Yasa aka lankaya ajikin wata bishiya, shi kuma ya kwanta karkashin bishiyar. Ruwan yana digowa ajikinsa saboda tsananin zazzabin da yake ji.
Sai nace "Ya Rasulallahi, da ka roki Allah ya yaye maka"
Sai yace "MAFIYA SHAN TSANANIN BALA'I DAGA CIKIN MUTANE SUNE ANNABAWA. SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU, SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU, SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU".
– Aduba MAJMA'UZ ZAWA'IDI juzu'i na biyu shafi na 392.
6. HAKURINSA BISA MUTUWAR 'YA'YANSA DA JIKOKINSA (Amincin Allah ya tabbata gareshi dasu baki daya).
Annabi (saww) ya shiga wajen 'dansa Ibraheemul Mu'azzam alhali alokacin nan yana jin jiki.. (ransa ya kusan fita).
Sai aka ga idanunsa (saww) suna zub da hawaye.
Sai Abdurrahman bn 'Auf (ra) yace : "Kai din ma kana kuka Ya Rasulallahi?!"
Sai Manzon Allah (saww) yace masa "YA KAI IBNU AWFIN, WANNAN (HAWAYEN) AI RAHAMA CE".
Sannan ya ci gaba da cewa : "HAKIKA IDANUWA SUNA ZUBDA HAWAYE, KUMA ZUCIYA TANA BAKIN CIKI. AMMA BA ZAMU FADI KOMAI BA, SAI DAI ABINDA ZAI YARDAR DA UBANGIJINMU.
HAKIKA MU MUNA BAKIN CIKIN RABUWA DAKAI YA IBRAHEEMU!!".
- Sahihul Bukhary hadisi na 1,303.
– Sahihu Muslim hadisi na 2,315.
* Hadisi na biyu awannan babin daga Sayyiduna Usamah bn Zaid (Allah shi yarda dashi tare da mahaifinsa) yace:
'Yar Manzon Allah (saww) ta aiko masa (shi Annabin) cewa : "Yarona Mutuwarsa tazo. Ina so kazo nan wajenmu.
Sai ya aika mata da gaisuwa tare da cewa:
"DUK ABINDA ALLAH YA KARBA, DAMA NASA NE. KUMA ABINDA YA BAYAR MA DUK NASA NE. KUMA KOWANNE ABU YANA DA WANI AJALI SANANNE AWAJENSA. KIYI HAKURI, KUMA KI NEMI LADANSA AWAJEN ALLAH".
Sai ta sake aiko masa tana magiya cewa DON ALLAH yaje. Don haka ya tashi ya tafi tare Sa'adu bn Ubaadah, da Mu'az bn Jabal, da Ubayyu bn Ka'ab, da Zaidu bn Thabit, da sauran mazaje (Allah shi yarda dasu baki daya).
(bayan ya isa gidan) Sai aka dauko masa yaron. Ya dorashi bisa cinyoyinsa (saww). Alhali shi yaron yana numfashi sama-sama. Sai idanun Manzon Allah (saww) ya fara zub da hawaye...
Sai Sa'adu bn Ubaadah (ra) yace : "Wannan menene haka Ya Ma'aikin Allah?".
Sai Manzon Allah (saww) yace masa "WANNAN (HAWAYEN) RAHAMA CE WACCE ALLAH YAKE SANYAWA ACIKIN ZUKATAN BAYINSA".
Awata ruwayar kuma cewa yayi "WANNAN RAHAMA CE WACCE ALLAH YAKE SANYAWA ACIKIN ZUKATAN WANDA YASO DAGA CIKIN BAYINSA.
KUMA MASU TAUSAYI NE KADAI WADANDA ALLAH YAKE TAUSAYA MUSU DAGA CIKIN BAYINSA".
- Sahihul Bukhary hadisi na 1,284.
– Sahihu Muslim hadisi na 923.
7. HAKURINSA BISA CHUTARWAR DA WASU DAGA CIKIN SAHABBANSA SUKAYI MASA (SAWW) :
* Yayin da aka kammala yakin HUNAINU, (An samo ganima mai yawan gaske ) Sai Manzon Allah (saww) ya fifita wasu daga cikin manyan sarakuna da shuwagabannin larabawa wajen rabon ganimar yakin.
Misali : Ya bama Al-Aqra'u bn Haabisin RAKUMA 100, ya bama 'Uyainah bn Hisnin shima haka.
Sai wani mutum (ana ce masa Dhul Khuwaisara At-Tamimiy) yace:
"WALLAHI wannan rabon ba'ayi adalci cikinsa ba!! Kuma ba'a nufi Allah cikin rabon nan ba!!".
Abdullah bin Amru bn Al-aas (ra) yana wajen. Sai yace "Wallahi sai na gaya ma Manzon Allah (saww).
Don haka naje na gaya masa duk abinda mutumin nan ya fada. Nan take sai naga launin fuskar Manzon Allah (saww) ya chanza. Yayi ja-jawur.
Sai yace : "SHIN WANENE ZAI IYA YIN ADALCI IN DAI ALLAH DA MANZONSA BAI IYA ADALCI BA?!
ALLAH YA JI-QAN ANNABI MUSA. AN CUCESHI FIYE DA HAKA AMMA YAYI HAKURI".
Aduba:
- Sahihul Bukhary hadisi na 3,150.
- Sahihu Muslim hadisi na 1,062.
ABIN LURA:
************
'yan uwa na tabbata duk wanda ya karanta darasin nan namu da kyau, kuma yayi tunani sosai, sai ya zubda hawaye.. Koda bakayi kuka afili ba, zuciyarka zatayi kuka saboda tausayinka ko soyayyarka ga Manzon Allah (saww).
Sannan ku dubi yadda ya rika hakuri yana nan ladansa awajen Allah (SWT). Tun daga kan jinyarsa har zuwa rasuwar 'Dansa da jikansa.
Ku dubi dadadan kalmomin da yake furtawa alokacin da idan mune zamu zama mun dimauci mun gigice, muna tunane-tunane kala-kala.
Manzon Allah (saww) ba ya rabuwa da jinya. Musamman ma ciwon kai da ciwon ciki. Kuma baya rabuwa da jarrabobi kala kala da kuma damuwa. Amma duk wannan ba ya hanashi Qiyamullaili, zuwa wajen yaki, fita domin gudanar da ayyukan alkhairi da jagorancin jama'a.
Sannan dukkan 'ya'yansa guda shida sun rasu ne agabansa.. Wasu ma akan hannunsa.. In banda Sayyidah Fatima (ra)..
Duk da yana da makiya masu yawa adoron Qasa, kamar Yahudawa da kuma Munafukan da suke cikin al'ummarsa, amma Manzon Allah (saww) bai ce ASIRI bane, ko MAKARU, Ko kuma wani abun makiyansa sukayi masa.
Muma ya kamata mu zam masu daukan darasi daga rayuwar nan tasa mai tsarki. Domin kuwa cikakken mabiyin sunnah shine mai koyi da halayen Manzon Allah (saww).
Amma aiki komai yawansa idan babu ikhlasi ba zai zama karbabbe ba. Hakanan kamanninka ko suturarka batta da wani tasiri awajen Allah sai dai abinda zuciyarka ta Qulle na alkhairi ko sharri.
Anan zamu tsaya sai karatu na gaba idan Allah ya kaimu.
Sallu alan Nabiyyi wa aalihi