Daga cikin Fa'idodin da ALBASA take Qunshe dashi, zamu gutsuro muku wasu 'yan kadan kamar haka:
1. Albasa tana tacewa jinin jikin 'Dan Adam. Duk mutumin da yake fama da matsalar Qarancin jini, ya yawaita cin albasa. insha Allahu jininsa zai yawaita.
Wanda yake fama da ciwon SICKLE CELL ANEMIA, ya rika yanka albasa tare da Ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu wannan ciwon Sickler din zai yi sauki.
2. MAGANIN TARI : Wanda yake fama da tari ko mura mai tsanani, ya nemi Man Albasa kamar cokali 9, zuma cokali 9.
A gauraya arika shan cokali uku bayan kowanne cin abinci. Insha Allahu Ciwon Qirjin zai warke, Kuma tarin ma za'a dena.
3. RASHIN YIN BAWALI : Wanda yake shan wahala wajen yin fitsari ko bahaya, Ka nemi Man albasa ka gauraya da zuma da lemon tsami. ka rika sha safe da yamma. kuma ka rika shafa man albasa ajikin Mararka. Insha Allahu zaka samu waraka cikin lokaci kankani.
4. CIWON SUGAR : Duk mai fama da yawan fitar fitsari saboda diabetes (Ciwon Sugar) ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci.
Insha Allah sugansa zai sauka, kuma zai dena yawan fita fitsarin.
5. ZUBEWAR GASHI : duk matar da take fama da zubewar gashi, ko kwarkwata, ko amosani, ta samu Ruwan albasa, Man Simsim, da kuma garin Baqadunas. ta rika shafawa a matsirar gashinta kullum kafin ta kwanta barci. idan ta farka sai ta wanke da ruwan zafi. ta ci gaba da yin haka har tsawon kwana bakwai.
Insha Allah zata samu waraka sosai.
DAGA ZAUREN FIQHU.