Wannan daurin kwalin yana daga cikin abubuwa mafiya hadari wadanda matan Zamanin nan suka tsiresu amatsayin ado.
Amma a hakika, wannan daurin kwalin yna janyo musu tsinuwar Allah da kuma azabarsa in har suka mutu basu tuba ba.
Manzon Allah ya riga ya fadesu tun fiye da shekaru dubu da dari hudu da suka wuce. Yace:
"AKWAI WASU NAU'I BIYU NA 'YAN WUTA WADANDA I BAN GANSU BA.
1. WASU MUTANE DAUKE DA BULALA KAMAR JELAR SANIYA SUNA DUKAN MUTANE DASHI.
2. WADANSU MATAYE, SUNA SANYE DA SUTURA AMMA TSIRARA SUKE. KARKATATTU NE, KUMA MASU KARKATARWA. (SIFFAR) KANSU TAMKAR TOZON RAKUMI.
BA ZASU SHIGA ALJANNAH BA, KUMA BA ZASU SAMU KODA QAMSHINTA BA. DUK DA CEWA ANA JIN KAMSHINTA TUN DAGA NISAN KAZA DA KAZA".
(Sahihu Muslim).
Imam Nawawy (rah) yace: Dalilin da yasa ba zasu samu shiga Aljannah ba, watakil saboda suna aikata wannan mummunar aikin ne duk da cewa Sun san cewa Allah ya hana. Amma suke yi. Saboda basu yarda da haramcin da Allah ya sanya akan hakan ba.
Rashin yarda da hukuncin Allah zai iya kai mutum zuwa ga kafirci. Kuma wannan shine dalilin shigarsu Wuta. Kuma ko Qamshin aljannah ba zasu ji ba..
Ya ku jama'a!! Ya kamata mu tashi tsaye wajen hana matayenmu, da Qannenmu da sauran danginmu daga yin irin wannan daurin kwalin da kuma mummunan dressing.
Ance wasu ma har Qunshin tsumma suke sanyawa acikin Kitsonsu!!! Allah ya kiyaye.