*********************************************
Kar kaga mutum yana aikata wani kuskure kaje kana ta zancensa ko gulmarsa, Ballantana kaje kana kafirtashi ko kuma kana zaginsa.
Yin haka zai iya janyo maka matsalar da tafi tasa girma awajen Ubangiji (SWT). Domin kuwa watakil shi wannan abinda kaga yana aikatawa iyakar aibunsa kenan.
Amma kai idan ka zageshi ko kayi gulmarsa, to ka aikata FASIKANCI kenan. Domin kuwa zagin musulmi fasikanci ne. Hakanan yin zancensa abayan idonsa kuma gheebah ne. wato kamar kaci namansa ne 'danye bayan mutuwarsa!!
Watakil shi idan yayi istigfari guda daya sai Allah ya gafarta masa. Amma watakil kai sai kayi fiye da shekaru talatin (30 yrs) kana istighfari amma Allah ba zai saurareka ba, saboda ka riga ka shiga hakkin bawansa. idan ba wannan mutumin ne kaje ka nemi gafararsa da gaggawa ba, to hakika kai din kana cikin hatsari.
Idan kuma kafirtashi kayi, watakil shi yana da hujjah bisa abinda yake aikatawa, watakil idan ma bashi da hujjar, to girman abin bai kai na kafirci ba... To kai kuma da ka fara kawo maganar kafirci, to kalmar ba zata rabu dakai ba. Mutukar shi din ba kafirin bane, to kalmar nan wajenka zata dawo ta sauka akanka. Kuma ba zaka fahimci cewa ka riga ka kafirta kanka ba, watakil sai ranar rasuwarka, alokacin fitan ranka... 'Yan uwanka suna jan kalmar shahada, suna so ka fadeta domin ta zam karshen furucinka, amma inaa!! babu dama!!!
Ka kasance masoyin dukkan Muminai, kaima sai Allah yaso ka.. ka Qudurce alkhairi azuciyarka tsakaninka da Allah da bayinsa. Sai ka zama Musulmi Mumini na kwarai.