Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sha alwashin samun galaba a kan dakarun da aka kafa domin yaki da su.
A wani sabon bidiyo da ya fitar, Shekau ya ce dakarun kawancen ba za su yi nasara ba duk da cewa sun yi shelar kafa runduna mai sojoji
fiye da 8,000.Ya ce dakarun makwabtan kasashe da suka shiga Nigeria domin yakar
Boko Haram sun yi kadan su iya samun galabar hana su gudanar da
ayyukansu.
Kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin sun
kafa rundunar kawance domin ganin an kawo karshen ayyukan Boko Haram da ya jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.
Rikicin Boko Haram ya janyo asarar rayukar dubban mutane a yayin da
fiye da mutane miliyan uku suka rasa muhallansu.
source bbchausa
Title :
Shekau ya yi wa dakarun kawance barazana
Description : Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sha alwashin samun galaba a kan dakarun da aka kafa domin yaki da su. A wani sabon bidiyo...
Rating :
5