Shahararren jarumin finafinan Hausan nan, Sani Musa Danja, ya jaddada goyon bayansa ga tafiyar Malam Salihu Sagir Takai, dan takarar gwamnan jihar Kano, a karkashin jam’iyyar PDP.Sani Danja ya ziyarci ofishin yakin neman zaben Takai daga kan titin Zaria a cikin birnin Kano, inda yayi alwashin bada duk wata gudunmawa da ta kamata don ganin Malam Takai ya lashe zaman gwamnan da za a gudanar ranar 11 ga watan Afrilu.Danja a baya na gaban Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne, wanda da shi aka yi yakin neman zaben gwamnan a shekarar 2011 har aka samu nasara. Haka kuma Jarumin yana daya daga cikin wakilan mashirya finafinai a kasar nan magoya bayan
tazarcen Shugaba Goodluck Jonathan.
…Ko goyon bayan Takai da Danja yake yi, zai
taimaka masa ya zama Gwamnan Kano, kamar yadda ya taimakawa Gwamna Kwankwaso?
Title :
Sani Danja Ya Jaddada Goyon Baya Ga Tafiyar Takai
Description : Shahararren jarumin finafinan Hausan nan, Sani Musa Danja, ya jaddada goyon bayansa ga tafiyar Malam Salihu Sagir Takai, dan takarar gwamnan...
Rating :
5