A yau Alhamis ne dai ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin
jam’iyyar hamayya ta APC Janal Muhammadu Buhari, zaiyi jawabi a
cibiyar manufofin harkokin kasashen waje da ake cewa Chatam
House, da turanci a birnin London. Ana sa ran zai tattauna da wasu
kososhin siyasar Birtaniya, kuma zai hadu da masu ruwa da tsaki
wadanda ke da sha’awa kan siyasar Najeriya.
Kan wannan tafiyar ta Buhari ce dai Aliyu Mustapha, ya tuntubi mai
baiwa shugaba Goodluck Jonatha shawara kan harkokin siyasa
Farfesa Rufa’I Ahmed Alkali, don jin ra’ayin jam’iyyar PDP game
wannan tafiya da Buhari yayi da kuma haduwa da shugabannin
siyasar turai da yake.
Farfesa Rufa’I yace, “wannan ba laifi bane ai tunda yake duk wanda
zai shugabanci Najeriya, yakamata ya zama shugaban kasa ne
wanda kuma dole ne yana da mutunci a idon duniya.” Ya dai ce basu
da wata damuwa game da cudanyar da shi Janal Buhari, yake da
shugabannin turai, kasancewer shima shugaban kasa dake kan mulki
Goodluck Jonathan, yana ire-iren wannan zagaya duniya.
Kuma duk wani mutum da yake neman siyasa babu inda baya
zagayawa domin neman jama’a, kuma ra’ayi na kasashen waje nada
muhimmamci ga ‘dan takara, daga karshe dai zabe a kasar Najeriya
za’a dawo ayi.
source dandali voa