Rundunar Sojin Nijeriya ta ce jiragen yakinta sun yi ruwan bama-
bamai a kan wani sansanin horas da mayakan Boko Haram da ke
dajin Sambisa a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar Sojin ta Nijeriya, Manjo Janar Chris Olukolade, ya ce
sun kuma kashe 'yan ta'addar masu dimbin yawa.
Sai dai kuma babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da
wannan ikirari.
Rundunar tace dakarun sojin kasashen Kamaru da Chadi da Benin da
kuma jamhuriyar Nijar, suna kokarin dakile ayyukan masu tada kayar
bayan dake iyakar kasashensu da Nijeriya, kafin su fara kai hare-hare
ta sama da kasa.
A bangare guda kuma Hafsoshin sojin kasashen za su gana a mako
mai zuwa a kasar Chadi domin shirya wadda za ta fisshe su kan hare-
hare ta kasa da ake sa ran dakarun hadin gwiwa 8700 za su
kaddamar.
Title :
(PICTURES)An kashe yan Boko Haram sama da 615
Description : Rundunar Sojin Nijeriya ta ce jiragen yakinta sun yi ruwan bama- bamai a kan wani sansanin horas da mayakan Boko Haram da ke dajin Sambisa...
Rating :
5