Wadannan matsaloli kuwa sune kamar haka:
(1) Malewa.
(2) Dadewa.
(3) fitar ruwa.
(4) Qurajen farji.
(5) Tsiron farji.
(6) kumburin farji.
(7) Doyin farji.
(8) Daskarewar ni'ima.
(9) cushewar farji.
(10) kaikayin farji.
Wadannan duk suna iya kama 'ya'ya mata.
Mata da yawa suna qorafi akan wadannan mas'aloli, saboda haka na rubutashi a fili domin kowa amfana.
1- Macen da take fama da qaiqayin farji sai tanemi wadannan abubuwa:
Tafarnuwa.
Garin hulba.
Man shanu.
Saita tafasasu ta dinga shiga tana zama sau uku a rana.
zata warke Insha Allah.
2- DADEWAR GABA:
Macen da take famada dadewar farji sai ta nemi wadannan abubuwa:
Ganyen kabewa.
Ganyen zogale.
Man kadanya.
Hulba.
Saita hadasu waje daya ta kwa6asu da mai ta dinga shafawa sau uku a rana duk shafawa sai ta wanke da ruwan dumi zataga biyan buqata.
3- MALEWAR FARJI:
Shine mace taji zafi in ana saduwar da ita taji kamar ciwone aciki to sai tanemi wadannan abubuwa:
Bagaruwa.
Alimun, amma dan kadan.
Ganyen zogale.
Tafarnuwa.
Saita cakudasu waje guda ta ringa zubasu a ruwa tana shiga.
Wannan zafin zai dauke Insha Allah.
4- DAUKEWAR NI'IMA:
Macen da ni'imarta ta dauke sai tanemi wadannan abubuwa:
Aya mai gishiri.
Gyada mai gishiri.
Gurjiya.
Madarar peak.
Nonon kucciya, wata ciyawace.
Saiki dakesu ki dinga shansu a madara ko nono ko kindirmo za kiga yadda ni'imarki zata dawo.
5- FITAR RUWA:
Macen da take fama da fitar ruwa sai tanemi wadannan abubuwa:
Saiwar zogale.
Saiwar rai dore, wato rai-rai wani icene mai kamada tafasa.
Garin tafarnuwa.
Barkono.
Daddawa.
Saiki hadesu kiyi yaji kidake ki tankade yai luqui, saiki dinga zubawa acikin abinci kina ci.
Sanyin ma da baki saniba zai fita daga jikinki.
6-QURAJEN FARJI:
Macen da take famada qurajen farji su suke haddasa in ana saduwa da ita taga jini ko ciwon mara.
Mai son maganin wannan sai ta nemi wadannan abubuwa:
Kaninfari.
Citta.
Kimba.
Zaki dake su ki riqa sawa a shayi ko ruwan dumi.
Darasi nagaba zaku ji ragowar bayanin Insha Allah.