Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage zaben da aka shirya za a gudanar ranar 14 da 28 na wannan watan.
INEC ta bayar da wannan sanarwar ce a wani taron manema labarai da hukumar ta yi a daren Asabar din nan, Shugaban Hukumar Farfesa Attahiru Jega ya ce, zaben shugaban kasa da na majalisun kasa za a yi ranar 28 ga watan Maris, sai kuma na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Afrilu.
Shugaba ya ci gaba da cewa, an dage zaben ne saboda rudunonin tsaro na kasa sun bayar da tabbacin cewa ba za su iya bayar da ingantaccen tsaro ba a ranakun da aka shirya na 14 da 28 a watan na Fabrairu.
Title :
HUKUMAR ZABE TA DAGE ZABE
Description : Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage zaben da aka shirya za a gudanar ranar 14 da 28 na wannan watan. INEC ta bayar da wanna...
Rating :
5