Janar Muhammadu Buhari, a yammacin yau, bayan kammala gangamin yakin neman zabe a jihar Gombe, ya gana da manyan ‘yan kasuwar jihar Kano, inda ya bayyana musu manufofinsa kan kasuwanci idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Wannan ganawa irin ta ce ta biyu, ko a jiya Janar Buhari yayi irin wannan ganawar a jihar Legas, inda nan ma ya bayyana musu manufofin na sa, sannan ya amsa tambayoyi 16 daga wajen ‘yan kasuwar.
Buhari zai ci gaba da irin wannan ganawa da masu ruwa da tsaki a fannoni daban – daban a fadin kasar nan kafin zabe, kamar yadda ofishin yada labarin na tawagar yakin neman zabensa ya shaidawa 1Arewa a daren jiya.
Title :
Buhari Ya Gana Da Manyan ‘Yan Kasuwar Kano
Description : Janar Muhammadu Buhari, a yammacin yau, bayan kammala gangamin yakin neman zabe a jihar Gombe, ya gana da manyan ‘yan kasuwar jihar Kano, in...
Rating :
5