Hawainiyarka Ta Kiyayi Ramar Ali Nuhu
Tabbas idan kana neman butulu na karshen idan ka samu Adamu A. Zango sai dai ka shafa fatiha ka tashi, saboda a tarihin butulci ban taba gani ko jin butulcin da ya kai wanda Zango yayi wa Ali Nuhu ba.
Idan maye ya manta uwar da ba zata taba mantawa ba, don haka idan ka manta ko waye Ali Nuhu to bari mu taimaka muyi maka tuni..:
Shine wanda yayi maka sanadin samun suttura lokacin da kake fakirinka almajiri duk da cewa Allah ya rubuta sai kayi arziki amma Ali Nuhu ne sila.
Shine wanda ya ciyar da kai da dukiyarshi da karfin shi, inda matarshi Hajiya (Aunty) Maimuna take kawo ma abinci kai tsaye da kanta ba aike ba duk saboda karamci da kirki irin nata da na mijinta, wanda ka ciwa mutunci.
Ali Nuhu ne yayi sanadin samun daukakarka da sunanka a duniya duk da Allah ya rubuta haka amma ta silar sa ka zama abinda ka zama.
Shi ne ya tsaya maka tsayin daka wajen ganin ka kafu da kanka ba tare da kyashi ko hassada ba, ba kuma da tunanin wata rana zaka iya zuwa ka yi gogayya dashi koma ka fishi ba.
A lokacin da fitinarka ta buwayi industry musamman tsakanninka da hukumar tace fina finan da rigimarka da wasu jiga jigan yan film Ali Nuhu na daga cikin wadanda suka tsaya ma ya hana idon shi bacci ya kasa zaune ya kasa tsaye wajen ganin ka samu kanka tare da sasantaku.
Haka kuma dai Ali Nuhun ne dai yayi sanadin kubutar da kai daga tarkon da abokina edita mujallar fim Aliyu Gora yaso saka a ciki sanadin rashin mutuncin da kayi masa, inda Ali Nuhu na daga cikin gaba gaban ganin an sulhuntaku kun zauna lafiya.
Duk wadannan abubuwan dama wasu da ban ambata ba idan kai ka manta mu bamu manta ba...amma da yake kai butulu ne mara tarbiya a yau wuyanka yayi kaurin fitsararka ta tsallake kowa ta dira akan Ali Nuhu bawan Allah.
Mutumin da ba a taba cewa ga abokin fadan shi ba a iya zaman shi a industry hatta Sani Musa Danja da yake babban abokin adawarsa har ya gama sharafinsa ba a taba jin kansu ba ba a taba ji ko musayar yawu sunyi ba.
Mutumin da kafatanin industry babu mai kima da mutuncin shi wajen daukar matasa aiki da kyankyashe sababbin jarumai kaman yanda ya kyankyashe ka.
Mutumin da har kawo yanzu ba a taba kama shi da wani abun Allah wadarai ba sabanin kai da Allah ya tsine a sati baka aikata abun tir da kyama.
Mutum me mutunci da sanin girman mutane tare da iya zama dasu. Mutumin da tunda yake ba a taba kama da wani abun rashin tarbiya ba babu wani dake aiki a karkashin shi ko kamfanin shi da baida kyakkyawar tarbiya sabanin naka yaran tatattu wajen iskanci mashahurai wajen rashin tarbiya, dakikai wajen rashin ilmi, sanannu wajen tabara da rashin ganin giman mutane, rikakkun 'yan daba 'yan tauri 'yan kalare 'yan sara suka ire iren su kaura ALI ARTWORK wanda ke garkame kaman barawo a hannun 'yan sanda saboda rashin ta idonshi...da kuma kaninka wannan mummunar yaron mai kama da 'yan sholi wato Kabiru Zango wa ya sani ma ko yana dan taba shan koken ko wani abun maye....
Tabbas a yanzu mun kara yadda da maganar malam bahaushe na cewa tsintacciyar mage bata mage kuma abinda ya baka tausayi wata rana zai baka tsoro wallahi ka cika rikakken mara mutunci cikakken butulu ga Ali Nuhu ka nuna ma duniya cewa kai dan kunama ne mai mugun dafi ka rasa wanda zaka sara sai wanda ya raine ka ya sha wahalarka wallahi kaji kunya.
Daga karshe muna shawartarka da babbar murya cewa ka yiwa kanka kiyamul laili, hawainiyarka ta kiyayi ramar ALI NUHU.
Daga
Saifullahi Lawal Imam
Marubuci
Memba Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA)
Sannan sakataren riko na Zazzau Literary Association
Title :
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Adam A. Zango Daga Saifullahi Lawal Imam
Description : Hawainiyarka Ta Kiyayi Ramar Ali Nuhu Tabbas idan kana neman butulu na karshen idan ka samu Adamu A. Zango sai dai ka shafa fatiha ka tashi...
Rating :
5