Biyo bayan sauya ranar zabe da hukumar INEC tayi, saboda jami’an tsaron Najeriya sunce baza su bada tsaro ba, jam’iyyun adawa sun fara kumfan baki, amma suna kira a kwantar da hankali.
Reverend Pinas Padio, kakakin jam’iyyar APC a Jihar Adamawa
“Babu yadda zamu tsorata, duk ranar da za’a ce zabe za’a yi, a shirye muke, mun sani ‘yan Najeriya, zasu bamu kuri’u, kuma zamu kafa gwamnati”
Mr. Padio ya cigaba da cewa “mu sako na farko, shine ga shugaban kasa da mukarrabansa. Mulki na Najeriya, ‘yan Najeriya ne suke badawa, bata wani hanya daban ba. Na biyu, ‘yan Najeriya suyi hakuri su tsaya bisa ga doka, kada su yarda su dauki doka cikin hannunsu.”
Reverend Padio nada sako ga hukumomi.
“Kuma hukumar zabe, da hukumar zabe su sani, Najeriya bata Jonathan bace, Najeriya ta ‘yan Najeriya ne. Saboda haka, suyi taka-tsan-tsan. Duk abinda zasu yi, suyi saboda biyan bukatun ‘yan Najeriya wadanda da kudadensu aka kafa wadannan hukumomi, kuma ake biyansu.
source voahausa
Title :
Baza Mu Tsorata Ba – inji APC
Description : Biyo bayan sauya ranar zabe da hukumar INEC tayi, saboda jami’an tsaron Najeriya sunce baza su bada tsaro ba, jam’iyyun adawa sun fara kumfa...
Rating :
5