An kai harin kunar bakin wake a babbar kasuwar Biu ta jihar Borno a Nigeria, lamarin da ya rutsa da mutane da dama.Wani shaida a hirarsa da BBC ya ce kasuwar ta cika makil lokacin da bam din ya fashe kasancewa abin ya fashe ne a lokacin da ake cin kasuwa.
Bayanai kuma sun nuna cewar an kama wasu mata biyu da ake zargin ‘yan kunar bakin wake ne a cikin kasuwar dauke da bama-bamai.
Wanda ya shaida lamarin ya ce fashewar ta auku ne da misalin karfe uku na rana kuma kawo yanzu babu adadin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata.Akwai dubban ‘yan gudun hijira a garin Biu na jihar Borno tun lokacin da ‘yan Boko Haram suka kwasa wasu garuruwan jihar.Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 tun daga shekara ta 2009.
bbchausa
Title :
Bam ya fashe a babbar kasuwar Biu
Description : An kai harin kunar bakin wake a babbar kasuwar Biu ta jihar Borno a Nigeria, lamarin da ya rutsa da mutane da dama.Wani shaida a hirarsa da ...
Rating :
5