APC TA ZARGI GWAMNATI DA SOJOJI DA SHIRIN MURDE ZABE
Jam'iyyar APC ta yi ikararin cewa, a halin yanzu gwamnati da kwamandojin rudunar sojan Nijeriya sun fara wani taron kwana uku a Kaduna wanda aka shirya shi don tsara yadda za a yi amfani da sojoji wajen murde zabe.
Shugaban jam'iyyar na kasa, John Oyegun ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai a yau a Abuja. Sai dai kuma rundunar soja ta fito ta musanta wannan zargi.
Da yake karin haske game da batun, Jami'ain yada labarai na rundunar soja ta kasa. Manjo Janar Chris Olukolade ya ce, "Ban da wata masaniya game da wani taro da ake yi tsakanin jami'an soja da 'yan siyasa. Abun da kawai na sani shi ne cewa, Kaduna yanki ne dake yawan gudanar da horo na soja a kai- a kai
Title :
APC TA ZARGI GWAMNATI DA SOJOJI DA SHIRIN MURDE ZABE
Description : APC TA ZARGI GWAMNATI DA SOJOJI DA SHIRIN MURDE ZABE Jam'iyyar APC ta yi ikararin cewa, a halin yanzu gwamnati da kwamandojin rudunar s...
Rating :
5