Dan takarar shugabanci Basalona Augusti Benedito yayi zargin cewa
kwamitin gudanarwa na kulab din na kokarin sayar da fitaccen dan
wasan ta Lionel Messi.
A halin yanzu shugaban Catalans mai ci yanzu Joseep Maria
Bartomeu, ya nuna ra’ayin sa da fatan cewar danwasan gaba na
Argentine zai kasance a sansanin Nou zuwa shekru da dama masu
zuwa.
Sai dai Benedito cewa yayi sakonnin dake fitowa daga kwamitin
gudanarwar Basa ya nuna cewar baza a iya yarda da shi ba.
A wata hira da ya yi ta musamman da mujallar Goal Benedito ya ce
“bayanan da suke fitawar a baina jama’a ba dai dai yake da ainihin
ra’ayinsu ba.”
Ya kara da cewa a wasu lokuta suna Magana da ta saba yadda suke
aiwatar da ayyukansu, ina fata a wannan lamari na Messi ba za a
samu haka ba.
Title :
An Zargi Kwamtin Amintattu na Basalona da
Yinkurin Sayar da Lionel Messi
Description : Dan takarar shugabanci Basalona Augusti Benedito yayi zargin cewa kwamitin gudanarwa na kulab din na kokarin sayar da fitaccen dan wasan t...
Rating :
5