Rundunar sojin saman Nigeria ta yi barin wuta a dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda ake zargin nan ne matattarar 'yan Boko Haram.
A wata sanarwa daga Manjo Chris Olukolade, rundunar ta yi ikirarin kashe mayakan Boko Haram da dama a luguden wuta da ta yi a dajin Sambisa da kuma wani yankin Gwoza.
"An yi barin wuta a yau da safe a Sambisa da yankin Gwoza kuma an samu nasara," in ji Olukolade.
A 'yan kwanakin nan jami'an tsaron Nigeria na ikirarin samun nasarori a kan Boko Haram amma kuma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin.
Hakan na zuwa ne bayan da dakarun Chadi suka kwato garin Dikwa daga 'yan Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram a cikin watan Yuli ta kwace garin Gwoza inda ta bayyana garin a matsayin daular Musulunci.
Source bbchausa
Title :
An yi luguden wuta a dajin Sambisa
Description : Rundunar sojin saman Nigeria ta yi barin wuta a dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda ake zargin nan ne matattarar 'yan Boko Haram. A w...
Rating :
5