Gwamnatin jihar Kano ta kamalla bai wa Sarkin Kano, Alhaji
Muhammad Sanusi II sandar girma a wani buki da aka yi yau Asabar.
Tun farko dai wakilin BBC a Kano Yusuf Yakasai ya ce fadar Kano ta
dau harami domin bikin nadin, kuma gwamnatin jiha ta gina wani
sabon dakin taro a gidan gwamnati wanda a ciki aka yi bikin nadin.
Wakilin na BBC ya kuma ce otal-otal na Kano sun cika da baki daga
sassa daban-daban na duniya.
An kuma yi wa fadar Sarki gyare-gayare na musamman domin bikin.
A ranar 8 ga watan Yuni aka nada Alhaji Muhammadu Sanusi II a
matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Sarki Ado Bayero a ranar 6
ga watan Yuni.
Wannan dai shi ne karo na farko da za a bayar da sanda ga sarki a
Kano tun shekarar 1963.
Source bbchausa
Title :
An yi bikin bai wa Sarki Sanusi sandar mulki
Description : Gwamnatin jihar Kano ta kamalla bai wa Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II sandar girma a wani buki da aka yi yau Asabar. Tun farko dai...
Rating :
5