Hukumomin tsaro a Jamhuriyyar Nijar
sun ce mayakan Boko Haram sama da
100 ne aka kashe a musayar wutar da
suka yi da dakarun kasar bayan sun kai
hari a garin Bosso da ke jihar Diffa.
Ministan tsaron Nijar Mahamadou
Karidjo ya ce ‘Yan Boko Haram 109 aka
kashe, amma akwai Sojoji hudu da
fararen hula da suka mutu a musayar
wutar da aka yi a jiya Juma’a bayan
Mayakan Boko Haram sun shigo garin
Bosso.
Wannan ne dai karon farko da Boko Haram ta kaddamar da
hari a Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.
Jami’an leken asirin Amurka sun ce Boko Haram ta fara shan
wahala saboda taron dangi da dakarun Chadi da Kamaru da
Nijar da Najeriya ke yi wa kungiyar.
Sai dai kuma Jami’an leken asirin sun ce Mayakan na Boko
Haram babbar barazana ce ga dakarun Najeriya saboda
makaman da suka kwasa a garin Baga.
A ranar Litinin ne dai Majalisar Nijar ake sa ran za ta kada
kuri’ar amincewa a tura dakaru domin yakar Boko Haram a
Najeriya.
Source: rfihausa
Title :
An kashe ‘Yan boko Haram 109 a Nijar
Description : Hukumomin tsaro a Jamhuriyyar Nijar sun ce mayakan Boko Haram sama da 100 ne aka kashe a musayar wutar da suka yi da dakarun kasar bayan ...
Rating :
5