Rahma sadau ta fito tayi Magana akan duk abin da ke kan faruwa a duniya finafinan kannywood. Ta yi wannan Magana ne tare da Dkudi, na hausa24.com
DKUDI:
Salam, na aiko miki da tambayoyi kan rikicinku da Zango… amma shiru ban ji daga gare ki ba
RAHMA:
Yaushe?
DKUDI:
Kwarai na turo miki sakon Tes, kwanaki biyu kenan. Na yi zaton bayan kin karanta, ba ki son cewa komai.
RAHMA:
Yi hakuri bari na duba wayar tawa.
DKUDI:
Amma tun da mun hadu a nan yanzu, me zai hana mu tattauna a gurguje? Da farko dai da yawa jama’a na ganin kamar akwai wadanda suka zuga ki, suka ruruta wutar rikici tsakaninki da Zango. Musamman suna ambatan sunan Ali Nuhu, mene ne hakikanin abin da ya faru?
RAHMA:
Gaskiya dai ba haka abin ya kasance ba! Shi Ali ma fada ya yi min, ya umarce ni da koma na ba wa Zango hakuri, don ba shi da hannu cikin rikicin.
DKUDI:
Mene ne ainihin abin da ya haddasa rikicin?
RAHMA:
Labari ne mai tsawo, ban sa ta inda zan fara ba, amma bari na takaita shi. Farkon farawa dai, wasu daga cikin yaran Zango, wadanda nake gani tsagera ne suka rika gugar zana game da ni, saboda na ki fitowa cikin fim din su. Hakan ya matukar bata min rai, shi ne ni ma na shiga yanar gizo na tura wa duniya wannan sakon (ta aiko min da hoton ainihin rubutun da ta yi a INSTAGRAM). Ga fassarar abin da ta rubuta da Turanci: “Me ya sa wasu ke ganin sun isa ne a wannan rayuwar? Ya kamata ka sani cewa tun kafin ka yi zarbabin sauke ni daga cikin fim dinka, ya zare kaina da kaina. Ban yi kama da wadda za ta rika binka da roko cewa sai ka sakata a cikin fim ba. Kin tayin soyayyarka ba zai cutar da ni da komai ba. Ni ce RAHMA SADAU, tuni Allah ya kai ni koluwar da nake hari ba tare da wani taimako daga gare ka ba ZANGO. Ba na bukatar mutane irinka su taimaka min a wannan sana’ar. Ina tare da Allah, da kuma wani jarumin maza da ya tsaya min, wanda kuma yake nufina da alheri a koda yaushe, wato ALI NUHU. Babu ruwana da irinka!!”
Daga baya, Ali Nuhu ya kira ni, ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan rubutun da na yi, nan take ya umarce ni da na koma na ba Zango hakuri. Shi ne na kara aikawa da wannan (ta kuma turo min hoton rubutun da ta yi mai dauke da nadama da ban-hakuri ga Zango), kamar haka: “… Hakika kuruciya ta debe ni har na aikata wani abu jiya, don haka nake ba wa Adam A. Zango da dukkanin jama’arsa hakuri bisa abin da ya faru, da kuma daraktocina, wadanda suka nuna min kuskurena…”
Bayan rubutun da na yi, sai da kira kowannensu a waya, duk kuwa da yadda wasunsu ke zagin nawa, amma na bada hakuri.
DKUDI:
Bayan haka, me ya koma faruwa?
RAHMA:
Bayan haka, na rika samun sakonnin barazana daga wasu yaransa, har ma wani dan’uwansa mai suna Rabi’u Zango yake cewa zai gamu da ni, kuma zai lalata min shagon da na bude kwanan nan. Ina Abuja, kwatsam, ‘yar’uwata ta kira ni ranar Lahadin nan da ta gabata, cewa sun je har shagon nawa, suka fasa, suka lalata min komai.
DKUDI:
Kin tabbatar cewa da gaske an lalata miki shago?
RAHMA:
Kwarai da gaske. Shi ya sa na shigar da kara. Yanzu haka ana ci gaba da binciken al’amarin.
DKUDI:
Lokacin da abin yake faruwa, kin sanar da hukumomin shirin fim?
RAHMA:
Kwarai ma kuwa, na sanar da shugabannin shirin fim, suka ce za su zauna a ranar 18 ga Fabrairun 2015 a kai.
DKUDI:
A iya tunaninki Rahma, mene ya haddasa wannan rikicin?
RAHMA:
Rashim fahimta ne kawai, sannan akwai wadanda suke da sauran jahilci. Yaran na Adamu, sun yi tunanin na zagi maigidansu ne, shi ne suka fara zagina, suke ta wadannan abubuwan.
DKUDI:
Amma kuwa an ce ke din ce kika fara zuwa har inda suke daukar fim, kika rika zagin Adamun tukunna har abin ya nemi ya gagari kundila…
RAHMA:
A’a… ba haka ba ne! Na dai je Zariya tare da wani yaron Adamun (Suleiman) kan wani zance ne daban, amma ba don na zagi Adamu ba, kuma har na bar wajen ma, ni ban gan shi da idanuna ba, an dai ce min yana cikin motarsa zaune.
DKUDI:
Amma kin ce Ali Nuhu ya umarce ki da ki ba Zangon hakuri, shin kin neme shi? Ko kuma tun da aka fara rikicin, ke da shi kun yi magana?
RAHAMA:
Duk kokarina ba mu yi magana ba, domin shi dai ba ya magana. Na yi ta kiransa shiru. Amma na aika masa da sakon tes.
DKUDI:
Daga karshe, mene ne fatan ki a yanzu?
RAHMA:
Ina son kowa ya kama gabansa, tun da akwai alamun wasu ba sa son a zauna lafiya. Ni dai Rahma Sadau ina kaunar zaman lafiya da kowa.
DKUDI:
Na gode.
Sorce: hausa24.com
http://hausa24.com.
Title :
“Ali Nuhu ya nuna rashin jin dadinsa kan rubutun da na yi” – Rahma Sadau
Description : Rahma sadau ta fito tayi Magana akan duk abin da ke kan faruwa a duniya finafinan kannywood. Ta yi wannan Magana ne tare da Dkudi, na hausa2...
Rating :
5