wannan mako ne wutar rikici ta tashi tsakanin jarumi adam zango da rahama sadau, wanda dalilin hakan ya faru bisa cire rahma da adam zango yayi a cikin fim din sa, inda ita kuma ta aika masa sakon zagi. Al’amarin da ya. Janyo kace nace a wannan tattaunawa ta mu da jarumi adam zango ya warware mana zare da abawa akan wannan abu, dalilin da ya sa ya cire rahama a fim dinsa, batun cewa da akai shima ya sa yaronsa ya zagi ali nuhu, kuma ya ce daga yanzu ba sauran maganar yaro da ubangida tsakaninsa da ali nuhu saboda ba zai iya tafiyar da ba gaskiya a cikinta ba.
Ku biyo mu don jin cikakkiyar hirar, inda farko mu ka fara tambayar Adam zango cewa Mun samu labari cewa ka fara daukar sabon fim dinka za mu iya sanin wanne ne?
Assalamu’alaikum warahamatullahi ta’ala wabarakhathu, sunana Adamu Abdullahi zango wanda ake kira Adam A. Zango ko kuma prince.
Yanzu haka ina daukar sabon shirina mai suna Duniya Makaranta, wanda nasiru ali koki ya kasance Frodusa, Falalu dorayi ne darakta.
Za mu so jin me ya faru aka chanza sunan rahama sadau a cikin wannan fim wanda tun farko aka shirya tana ciki.
Dalilin da ya sa na chanza Rahama sadau a cikin shirina mai suna duniya makaranta ba wani abu bane. Dama tun farko ban taba yin fim da ita ba, tun daga lokacin da na taba gayyatar ta fim dina mai suna Nas, za ta fito min a wani rol da za ta yi waka guda daya kuma ta fito a sina sinai uku.
Na tura har gida aka sameta saboda ina bukatar sabuwar fuska, A wannan lokacin wanda na tura sai ta gaya masa cewa ita ba ta son ta fara yin wani fim a industiri har sai ta fara fim din FKD. Saboda haka ta yarda za ta yi fim dina amma kuma ba zan saki wannan fim din ba har sai tayi fim din FKD ya fita kasuwa, Ni kuma na ga banga dalilin da zan yi amfani da kudi na don kaina kuma in bari wai har sai ta yi fim a FKD sannan ni zan sake fim dina ba. Saboda a wannan kokacin nine zan taimaka mata ba ita za ta taimaka min ba.
A wannan lokacin sai nace to na cireta kuma raina ya baci sosai, har na yi furucin cewa insha Allahu har ta gama Career ta a cikin masana’antar fim ba zan yi fim da ita ba, koma waye ya kawo min ba zan yi ba.
To tun daga wannan lokacin sai ya kasance ta na ta yin films amma ba ta taba yin fim da ni ba.
Saboda haka sai ya zamana ‘yan kallo masoyanta su na requesting ta yi fim da Adam zango, Sai ya zamana ni kuma a wannan lokacin kowanne frodusa Idan ya dauko fim zai hadani da ita kafin ya kawomin zai hadu da wanda zai gaya masa cewa Aa idan fa ka kai wannan fim din Adamu ba zai yi ba saboda ya ce ba zai yi fim da ita ba. Saboda haka frodusa kafin ya kawo ma sai ya chanzata. To sai wannan abun ya yi effecting dinta (taba ta).
To da taga abun ba mai daidaituwa bane da kanta rahama ta gayyaceni ya kai akalla sau uku ba mu samu zama ba, daga baya sai Nace bari na saurari yarinyar nan na ji mai ta ke tafe da shi.
Inda mu ka zauna ta sanar da ni cewa burinta a rayuwarta shine tayi fim da ni, ta yi fina finai amma ta na ganin Career din ta bai cika ba har sai ta yi fim dani. Har ta bani misali da wata a indiya wanda ta yi fina finai da dama da jarumai amma ba taba yin fim da ko salmankhan ne ko sharukahn ne ba zan iya tunawa ba. Tace To wannan mata ta shiga kafar yada labarai inda ta ce burinta bai cika ba, saboda haka ita ma rahma ta na ganin career ta ba zai taba cika ba har sai ta yi fim dani. Sai na ce mata to ai ni bana rejecting fim da ita, tace a’a an gaya mata ina rejecting. Na yi mata rantsuwa nace wallahi ban taba rejecting fim da ita ba, saboda haka a wannan lokacin na ce mata idan kina tunanin ina rejecting fim da ke, na yi miki alkawari zan dauko daya daga cikin script dina zan sanya ki a ciki mu fito ni da ke, A wannan lokacin na yi casting dinta a fim dina DUNIYA MAKARANTA ba tare da na fada mata sunan fim din ba.
To bayan na zo na fara shiryen fim din sai na yi fosta ban sanar mata ba, domin na yi mata suprise ta gani kawai a social network, kawai ta ga fostan ta da Adamu Zango bayan ba ta taba tsammani ba. To da na yi wannan fostar sai na saka a instagram, Sulaiman ya saka akalla mutanena sama da mutum goma duk sun saka.
Mu na haduwa da ita washegari za mu yi wata tafiya zuwa bikin gidan sarki, sai na ke yi mata magana akan za fa mu kara wata waka HALWA a cikin fim din DUNIYA MAKARANTA. sai yarinyar nan ta nuna ba ta ma san wani labarin wani fim ba, sai abun ya bata min rai, ya zan yi miki suprise, Duniya ta gani ma ta na cewa bari mu ga mai za su fito mana da shi, ‘Yan rawa da ‘Yan rawa sun hadu, sai raina ya baci sai ban yi mata magana ba amma sai na gayawa duk wanda ya dora wannan fostar a internet to ya cire. To daga nan kawai na cireta.
Ya kaji da irin maganganun ko muce ya kake kallon zagi da rahamar ta yi ma bisa wannan dalili?
Wato magana ta gaskiya alokacin da rahama ta tura zagi da ta yi min akan instagram raina ya baci sosai, amma na yi kokari na yi controlIng din temper dina, saboda kada ya zamana cewa na koma karkashinta a maimakon ni da na ke babba gareta, sai ban yi magana ba, bance mata komai ba, kuma ban baiwa kowa izinin ya yi mata magana ba.
Saboda abun da na sani shine na taso a masana’antar fim babu wanda na raina, babu kuma wanda zai ce Adamu zango yau ya zage shi ko kuma yayi masa rashin kunya kwatankwacin irin wanda rahama ta yi min.
Amma dai abun da na sani raina ya baci kuma abin da ya zo tunanina shine Rahama ba ta isa ta yi min wannan zagin a karin kanta ba, Dole sai WANI ya sa ka ta. Ko WASU sun sa ka ta. Saboda haka wannan dalilin ya sa nace to Rahama ba sa’a ta ba ce ba zan yi rigima da ita ba, Amma duk WANDA ya sa ka ta ko wadanda su ka sanyata su fito fili su yi dani kai tsaye sai mu buga da su koma su wanene.
Wannan dalilin ya sa ban kula ta ba, wanda kuma hakan har ya jawo kananan surutai daga wurin masoyana ko kuma ince masoyana suka zamana cewa su na gaya mata maganganun da babu dadi ita ta janyo duk wata matsala da ta faru bisa wannan zagina da ta yi.
Amma ni na sani cewa ina da shaidu a masana’antar fim cewa ni Adam Zango ba marar kunya ba ne! Ni Adam zango ina girmama na gaba da ni! Wanda ya riga ni shigowa ko da na girmeshi ina ba shi girma a matsayin (senior) na.
Kuma duk daukakar da Allah ya bani ban taba amfani da ita wajen musgunawa wani kan cewa bai kaini ba ko wani abu. Abun da na sani shine ni mutum ne mai principles da kuma tsari wanda na ke ganin za taimaki career ta.
Wanda hakan ya janyo min makiya da magauta a masana’antar fim industiri. Wanda hakan su na ganin laifi ne a wurinsu sabo da Na ce sai na yi kaza sai anyi kaza zan yi fim ko sai an biyani abu kaza!
Wannan dalilin ya sa kashi tamanin da suke cikin masana’antar fim ba sa sona, kuma yau da idan da zan mutu za su yi farin ciki, cikinsu kashi ashirin ne su ke son ci gabana kuma su ke so na, suma ba su da wani dalili da za su ce gashi mu na son adamu ne sabo da kaza! Aa, sannan ni abun da na sani Allah ya bani rufin asiri ne domin In taimakawa mai neman taimako wanda bai fi karfina ba, wanda ya fi karfina kuma ba na iyawa.
Saboda haka abun da rahama ta yi min na barta da sa’ointa ko kuma ince na barta da mutanen gari wanda za su yi alkalanci akan ba su taba ganin irin wannan kalmar a wajen adamu ba don haka Adamu bai chanchanta rahama ta yi masa wannan abun ba.
Akwai wani mai suna ali artwork da ya zagi ubangidan rahamar bisa takaicin abin da ta yi ma, me nene gaskiyar cewa a ake kai ne ka sanya shi?.
Wallahil azim! Billahil lazi la’ilaha illa huwa. Ban saka Ali artwork ya zagi ali nuhu ba. Abun da na sani kawai shine Ali artwork yaro ne mai biyayya, dari bisa dari. wanda komai zai iya yi adalilin in anci nutuncina ko an taba ni wannan dalilin ya sa ya ga cewa an zageni amma babu wani babba a fim industiri da ya yi kwaßa ko ya nuna abun da yarinyar ta yi bata yi daidai ba.
Wannan abun ya sa ya harzuka ya ga tun da ba ayi magana ba kenan ubangidansa ya zama mutumin banza ne kenan ba kowa ba ne shi a industiri, shi ya sa shima ya shiga yayi magana akan ubangidanta kamar yadda ta yi magana akan ubangidansa.
Ba Ali artwork kawai ba akwai yara da yawa a karkashina wanda su ka yi niyyar zagi kamar yadda ta yi, da naga wanda ali artwork ya yi, na yi sauri na kwabe su nace duk wanda ya yi ba da yawu na ba, ban yafe masa ba, saboda haka suka cire abubuwan da suka fara yi, kuma daga wannan lokacin babu wani da ya kara fadin wani mummunan abu akanta ko kuma ubangidanta.
Saboda haka ni ban saka shi ba amma duniya ta dauka cewa ni na saka shi, wanda hakan ba daidai bane. Bai kamata ace a fim industiri an mayar da ni tamkar cewa ni ba kowa bane! Bayan nine mutum na farko ko na biyu ko na uku wanda ya ke kawo cigaba a masana’antar fim da chanji. Saboda haka bai kamata na zama wani bare ko kuma in zamo wani mutum da ake kin sa ba, wanda wannan dalilin ya sa har irin su rahama sun samu damar da za su yi irin wannan cin mutunci a gareni.
Akwai wani mataki ne da ka ke tunanin dauka a hukumance bisa ga abin da rahamar ta yi ma?.
Babu wani mataki da zan dauka akai abun da na sani dai kawai shine, nima ina da sako da aka turo min cewa za ayi min mummunan abu wanda a cikin tes din abun da aka rubuta shine “kai wawa da kai da jakunan abokanka ba ka isa ka yiwa yallabai komai ba, ba don yallabai ya hanamu ba to da aka za mu dauko ka mu kawo ka wurinshi, to amma a cigaba watarana za ka gane kurenka. kuma ka saurare mu za mu rama.” Wannan shine abun da aka rubuta a cikin tes din. Wannan shine kawai matakin da na dauka na jeni na ajiye shi pending a state C.I.D ko da wani abu ya biyo wannan.
Saboda haka Ni ban dauki mataki yanzu ba amma wannan tes din shi zai bani dama na dauki wanda ba ma irin wanda su ka dauka akan yarona da su ka kulle shi kwana uku a police station, ba tare da shugabannin mu ‘yan fim ko kuma wasu sun shiga sun gano cewa a’a menene ya sa Rahama ta yi zagi Adamu Zango bai kamata ba, amma Ali Artwork ya yi zagi Ali Nuhu ya kama shi.
Bayan nan akwai yaro mai suna cash money wanda shima yaron ali ne yaron fati Muhammad da alin da fatin su ka saka aka kama yarana mr bangis da kuma kanina Rabi’u saboda ransu ya baci sunce sai sun yi masa duka da sauransu. Su ka je su ka yi sharri wai sunce za su kashe shi aka kai su police station.
Bayan wannan akwai shago wanda ba mu san wanene ya je ya ballawa rahama sadau fostar shagonta ba wato banner kenan. Su ka dauka (still) su ka kai yarana police station akan maganar cewa an fasa mata shago ana mata barazana.
Duk wannan su kadai su ke yi ni ban dauki wani mataki ba, duk da ina da hujja mai karfi da zan iya daukar mataki. Don haka abun da na ke son sanar da jama’a.
Yau rana ce da zan fadi abun da Al’umma ba su sani ba shine wanda su ke min kallon cewa ni yaro ne a wurin ali. Wannan kalma mai suna yaro a wurin Ali nine na dauka na dora masa, na kuma ce shi ubangidana ne.
A shekara goma sha hudu da na ke fim industiri a lokacin da ali nuhu ya sameni na zama Adam Zango sunana ya yadu a duniya, duk kida mai sunan kida wanda duniya ta san da shi daga Kan yakubu Muhammad, Abubakar sani, sadi sidi sharifai, Mudassir Kasim, Adam kirfi , Adamu nagudu. Da dai sauran duk wasu mawaka wanda su ka kasance mawaka ne da suka amsa sunansu da ni suke kida a wannan lokacin, kuma sunana ya shiga duniya fiye da yadda mutane su ke tsamani.
A wanchan lokaci na yi yunkurin mutane da dama ko kuma produsoshi su sakani a fim, amma a wannan lokacin ba wanda ya kulani har sai da na tara kudi, da kaina na yi wa kaina fim mai suna surfani, har na sake shi a kasuwa, inda a wannan lokacin ne frodusoshi irin su bauni, irin su Ali, irinsu najjashi Sb jakara, suka ga wannan fim din suka ga cewa wannan yaron ya na da talent za mu iya saka shi a fim dinmu. A wannan lokacin (yes) ni ba kowa ba ne duniya ba ta sanni a fuska ba, amma ta san sunana, a wannan lokacin ne Najjashi sb jakara ya yi min fim MISALI, Bauni yai min DUKIYA, Ali nuhu yai min ZABARI. Sabo da haka a wannan lokacin wadannan mutanen sai na dauke su a matsayin iyayen gidana, amma me sai na fi fifita Ali akan su.
Saboda a wannan lokacin ina ganin shine ya yimin fim din da a wannan lokacin duniya ta fi gane ni don ya fi fim dina karbuwa a duniya. Wannan dalilin ya sa na dauki suna na bashi na matsyin mai gidana ba wai don wani abu ba.
Amma na zama wani sunana ya bazu a duniya kafin ya sani a fim dinsa, don haka wannan (credit) ne da na bashi saboda kyautatawa da ya yi min.
Saboda haka ina so duniya ta sani cewa ni na yiwa kaina komai a masana’antar fim industiri kafin wani ya taimakeni, don haka na fadi wannan ne ba don komai ba sai don na wanke kaina wurin wadanda su ke tunanin cewa ali nuhu shi ya kawoni ko kuma shine mutumin da yayi min wani abu a masana’antar fim.
Saboda haka abun da na ke so in kara fada anan shine, na kasance na yiwa ali nuhu biyayya, sama da shekara goma sha biyu, Allah ya kaini wani matsayi sahu irin nasa. Duk inda naje za ace ga adamu zango ga ali nuhu, amma hatta in tafiya za mu yi ni nake daukar jakar ali nuhu in rike, idan ina tare da wanda ni kuma ya ke tafiya tare dani, sai ni kuma Ya rike tawa jakar, idan ina zaune ali nuhu ya zo guri zan tashi ya zauna a wurin, idan zan yi wani abu a wannan wurin wanda shi ali a wannan wurin ba shi da damar yi ni zan yi masa.
Amma duk da haka yaran da ke zagaye da ali babu wanda ba ya cin mutuncina , ba ya raina ni ba ya wulakanta ni yadda ya ga dama, wanda hakan na yiwa ali nuhu complain ba adadi, ya yi musu fada amma kuma babu wanda ya gyara dabi’unsa.
Ni kuma na rantse da Allah a cikin kanne na da mu ke uwa daya uba daya, da yara da ke karashina babu wanda ya isa ya zagi ali nuhu ya zauna lafiya tare dani, su sun san wannan, su ma shedu ne a wurina.Don haka ni ban ga dalilin ni ina girmama shi, yarana na girmama shi, amma shi kuma ba zai kasance yaransa su girmama ni ba, Saboda haka tafiyar ba ta da amfani mu cigaba da tafiya mu na munafuntar junan mu da sauran su.
Ina da yaran da su ke girmamani su ke jin haushin abin da yaran ali su ke yi min, kuma su ke niyyar daukar mataki amma ni na ke hana su, sama da shekaru da dama. Allah ya sani ina da mabiya da za su daukar min mataki kowanne iri ne, amma ban taba supporting (goyon baya) ayi violence (tashin hankali) ko ayi wani abu na cin mutunci ba, kuma har abada ba zan yi goyon baya ayi hakan ba.
Amma abun da na ke so na sanarwa duniya yau shine! Ni da Ali Nuhu yanzu musulmai ne dukkan mu, sannan jarumai ne , kuma ‘yan uwan juna ne na musulunci.
Amma daga rana mai kamar ta yau ni da ali nuhu sunanmu jaruman hausa fim industirin hausa amma dangantakar da suka sani tsakani na da shi ni na yanke ta.
Saboda Allah ya gani na kai masayin da zan iya tsayawa da kafata tun shekara goma da ta wuce, Na godewa Allah abokanan da na taso da su tun bani da komai, tijjani asase, falalu dorayi, Tahit I. Tahir, baban chinedu, Adam m. Adam, marigayi kaura har kaura ya koma ga Allah mu na tare da shi, akwai wadansu ma da jama’a ba su san su ba, sun taimaki career ta, sun taimaki rayuwata lokacin da nake dan karami ba zan iya kula da kaina ba.
Abun da na sani wadannan mutanen ina nan tare da su, su na zagaye da ni. Kuma suna taimakona mu na samun sabani kuma muna shiyawa, amma har yanzu ban chanza su ba. To na gode wa Allah da wannan mutanen da ya bani da suke protecting dina da taimakon Allah sun isheni.
Ba zan iya rayuwa wadda za ace akwai munafurci a cikinta ba, babu girmamawa duk abun da za ayi ya zama I- service ni ban san shi ba, kuma ba zan yi ta ba. Saboda haka ina so mutane su sani cewa idan abun da na aikata ko kuma na yi kuskure a cikin maganganu na su gafarceni.
Kuma yan uwana maza da mata na cikin fim industiri shine, na ke so su sani cewa yau idan mune gobe ba mu bane ba, yau idan ana yayin Adam A A. Zango gobe ba shi bane ba, idan babu tsufa akwai mutuwa, to su yi hakuri duk randa Allah ya yi zai dau rai na ko kuma zai dauke daukakar da yi min daga kaina su huta da gani na ballantana su rika yi min muggan kalamai da kuma batanci a duniya.
Wanda Allah ya gani ya sani ban taba kwana da wani jarumi ko jaruma ko frodusa ko darakta a zuciyata ba, aa ba adamu ba ne wannan, ba na kuma fatan na kwanta da tunanin wani ya tare min wani abu a duniya.
Daga karshe ina fatan maganganun da na yi idan na batawa wadanda su ka karanta ko su ka saurara su gafarceni, Allah ya baiwa kasar mu zaman lafiya ya kuma taimaki addinin musulunci na gode.
Toku jama’a meza kuce game da wannan maganar?