Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan Boko Haram sun saki mata kusan 200 cikin wadanda suka kama a farkon watan nan.
An kama matan ne dai a kauyen Katarko da ke Gujba lokacin da 'yan Boko Haram suka kai hari, kana suka kashe maza da dama.
Wani jami'in garin ya shaida wa BBC cewa an saki mata kusan 200 a cikin 250 da Boko Haram ta kama.
A cewarsa, "Sun saki matan ne bayan sun tambaye su idan suna so su bi su wajen daukaka kalamar Allah, amma matan suka ce ba sa son zuwa. Daga nan ne suka dauke su zuwa wani kauye suka ajiye su.
Sun shaida musu cewa tunda ba za su bi su ba, to su je su bi dagutai. Daga nan ne muka tura motoci suka je suka dauko su".
Ya kara da cewa an kwaso mata 152 ranar Juma'a yayin da aka kwaso 73 ranar Asabar.
Ya ce har yanzu akwai ragowar mata da kananan yara kusan 30 a hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.
Source bbchausa
Title :
Yan Boko Haram sun saki mata kusan 200
Description : Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan Boko Haram sun saki mata kusan 200 cikin wadanda suka kama a farkon watan...
Rating :
5