IDAN 'YAN ALJANNAH SUKAZO SHIGARTA, MALA'IKU ZASU YI MUSU KIRARI SUNA CEWA:
Amincin Allah ya tabbata gareku, Kunji dadinku, zaku zauna acikinta, Zama ne na dawwama Batare da Mutuwa ba.
Kun samu Samartaka (Ta har abada) ba tare da Tsufa ba.
Kun sami Arziki wanda babu talauci bayansa.
Kun sami lafiya (ta har abada) ba tareda Jinya ba.
"Kun samu farin ciki wanda babu Bakin ciki bayansa"
Allah yasa da NI da KU, da Iyayenmu, da iyalanmu, da dukkan Masoyan Annabi muna cikin 'Yan Aljannah.
Albarkacin rahamar da Allah yake saukarwa domin darajar Muhammad Rasulullah.