KO KA/KIN TABA SAMUN IRIN WANNAN JARRABAWAR DAGA ALLAH ???
¤====¤ ¤=====¤ ¤===¤
ACIKIN AL'UMMAN DA SUKA GABACEMU DAGA BANI ISRA,IL ANYI WASU MUTANE GUDA UKU KAMAR HAKA:
1. DAYA KUTURU
2. DAYAN MAKAHO
3. DAYAN MAI CUTAR KORA {RASHIN GASHIN KAI MAI KYAU}.
SAI ALLAH YAI NUFIN YA JARRABA SU, SAI YATURO MUSU MALA'IKA ACIKI SIFFAR DAN ADAM.
SAI MALA,IKAN YAFARA ZUWA GURIN KUTURUN.
SAI {MALA,IKAN} YACE DA KUTURUNNAN, KAI KUWA ME KAKESO ADUNIYAR NAN ?
SAI KUTURUN YACE, AINI BA ABINDA NAFISO KAMAR NAGA NASAMI LAUNI DA FATA MAI KYAU KUMA DUK WANNAN KUTURTAR TATAFI DAGA GARENI.
SAI MALA'IKANNAN YA SHAFESHI, SAI GASHI YA DAWO KYAKKYAWAN MUTUM MAI KYAKKYAWAN LAUNI DA FATA MAI KYAU.
SANNAN SAI MALA'IKAN YAQARA CEWA A DUNIYA KUMA ME KAFISO ?
SAI YA CE RAKUMI.
SAI KUWA MALA'IKAN YAKAWO MASA TAGUWA {MACEN RAKUMI} MAI CIKI, SANNAN YACE ALLAH YAI MATA ALBARKA.
DAGANAN SAI YATAFI WAJEN MAI KORA, SAI YACE DASHI KAI KUWA ME KAFISO A DUNIYARNAN ?
SAI MAI KORAR YACE AINI BABU ABUN DA NAFISO SAMA DA KYAKKYAWAN {BAKIN} GASHI KUMA DUK WANNAN KAZANTAR TARABU DANI.
SAI MALA'IKAN YA SHAFESHI SAI GASHI YADAWO TSAF DA KYAKKYAWAN GASHINSA.
SAI MALA'IKAN YACE MASA TO ME KAKESO KUMA NA DUKIYA ?
SAI YA CE SANIYA.
SAI MALA'IKANNAN YAKAWO MASA SANIYA MAI CIKI SANNAN YACE ALLAH YAYI MATA ALBARKA.
DAGANAN SAI YA TAFI GURIN MAKAHO, SAI YACE DASHI KAI KUWA ME KAKESO ADUNIYARNAN ?
SAI MAKAHON YACE AINI BABU ABUN DA NAFISO SAMA DA ALLAH YA DAWOMIN DA GANINA KAMAR KOWA.
SAI MALA'IKANNAN YA SHAFESHI, SAI GASHI ALLAH YA DAWO MASA DA GANINSA.
SAI MALA'IKAN YACE TO ME KUMA KA KE SO NA DUKIYA ?
SAI YACE QANANAN DABBOBI.
SAI YA KAWO TUNKIYA MAI CIKI YA BASHI, KUMA YACE ALLAH YAYI MATA ALBARKA.
SAI BAYAN AN KWASHE LOKUTA MASU YAWA BAYAN KOWANNE DAGA CIKINSU YATARA GARKE NA DABBOBI MASU YAWA KOWA DAGA CIKINSU YA FASO GARI.
SAI GA MALA,IKANNAN YADAWO SAI YAFARA ZUWA WAJEN KUTURUNNAN, MALA'IKAN YAZONE A SIFFAR KUTURU SAI YAYI SALLAMA DASHI.
DA YAFITO SAI MALA'IKAN YACE DASHI, BAWAN ALLAH NI MATAFIYINE KUMA MISKINI GUZIRINA YAQARE ABIN DAYAKE WAJENA BAZAI ISHENIBA
SABODA HAKA DA ALLAH NA DOGARA SANNAN DAKAI.
INA ROKONKA DAN WANDA YABAKA LAUNI ME KYAU KUMA YA BAKA FATA MAI KYAU KA TAIMAKA KABANI RAKUMI DAYA WANDA ZAI ISHENI AHALIN TAFIYATA.
SAI KUTURUNNAN YACE:
KAI! AMMA WANNAN ABIN DAKA TAMBAYA YAYI YAWA.
SAI MALA'IKAN YACE HABA BAWAN ALLAH, NIFA KAMARMA NA SHEDAKA, BAKAI BANE KUTURUNNAN WANDA DAGA BAYA ALLAH YABAKA LAFIYA KUMA TALAKA, ALLAH YA BAKA ARZIKI ?
KAWAI SAI KURUNNAN YACE, BA HAKA BANE KUMA WADANNAN RAKUMAN DAKA GANI GADONSU NAYI A WAJEN KAKA DA KAKANNINA.
SAI MALA'IKAN YAYI MASA ADDU,A YACE:
"YA ALLAH INDAI QARYA YAFADA TOKA MAI DASHI YADDA YAKE ADA!"
YANA GAMA ADDU'AR NAN KAWAI SAI FILIN KUTURTA KUMA TADAWO.
DAGANAN SAI YATAFI WAJEN MAI KORA, SHIMA ACIKIN SIFFA IRIN TA MAI KORA.
SAI YA TAMBAYESHI KAMAR YADDA YA TAMBAYI WANCAN.
SAI SHI MAI KORAR YAFADI KAMAR YADDA WANCAN KUTURUN YAFADA.
SAI MALA'IKAN YACE YA ALLAH INDAI QARYA YAFADA TO ALLAH KAMAI DASHI YADDA YAKE ADA SHIMA KUWA ANAYIN ADDU'AR SAI FILIN KORAR TADAWO.
DAGANAN SAI YATAFI GURIN MAKAHO, SAI YACE MASA, NI TALAKANE KUMA INA HALIN TAFIYA AMMA GUZIRINA YAQARE BABU ABIN DA ZANYI GUZIRI DASHI, INA ROKONKA DAN GIRMAN WANDA YA DAWO MAKA DA GANINKA KA TAIMAKA KABANI TUNKIYA GUDA DAYA WACCE ZANYI GUZIRI DA ITA.
SAI MAKAHONNAN YACE, ALLAH SARKI KAGA NIMAFA ADA MAKAHONE SAI ALLAH YA DAWOMIN DA GANINA.
DAN HAKA ZO MUJE KADUBA DUK TUNKIYAR DA TAIMA KA KAMA NABAKA DAN ALLAH.,
SAI MALA'IKAN YACE:
RIKE KAYANKA DAMA JARRABAWA AKAI MUKU, HAKIKA KAI ALLAH YARDA DAKAI SU KUMA RAGOWAR ALLAH YAYI FUSHI DASU.
{BUKHARI DA MUSLIM SUKA RAWAITOSHI}.
DOMIN QARIN BAYANI KUDUBA LITTAFIN RIYADUS SALIHIN BABUL MURAQABATI: HADISI MAI LAMBA 65 SHAFI NA 23-24}.
YA ALLAH MUNA ROQONKA DUK JARRABAWAR DA ZAKAI MANA KABAMU IKON CINYEWA.