1. AADAWA (mutanen Annabi Huud a.s.):
Yayin da Manzo yaje musu da gargadi daga Ubangijinsu sai sukayi girman kai suke ganin cewar:
Su sunfi Qarfin wani mutum yayi musu wa'azi.
WAI DON ME BA ZA'A TURO MUSU MALA'IKU BA!!!
Saboda Qarfin jiki da da kuma Girman halittar da Ubangijinsu yayi musu.
Sai sukayi jayayya da ayoyinsa, suka Qaryata Manzanninsa, suka bi son zuciyarsu.
Daga Qarshe sai Ubangiji ya tura musu wata irin iska daga gareshi MAI QARFIN GASKE, mai tsananin Sanyi.
Har tsawon Darare Bakwai da wuni Takwas wannan Masifaffiyar iskar tana bugawa akansu.
Ta rurrushe gidajensu da katangun da suka kewaye garin dashi, Sannan ta Tsintsinke Kayuwansu, Tayi rugu-rugu da gangar jikinsu, nan ta barsu ayayyashe tamkar guma-guman bishiyoyin dabinai..
Allah yana bamu labarinsu ne domin mu wa'azantu mu gyara halayenmu karmu aikata irin laifukansu.
Tabbas Girman - Kai sutura ce ta ALLAH.
Allah ya riga ya rantse cewa duk mutumin daya ara ya yafa, to saiya Qaskantashi ya azabtar dashi.
Allah ka rabamu da girman kai.