Mayakan Boko Haram sun sace mata da kananan yara kusan
200 sannan kuma suka kashe mutane fiye da 30 a wani
kauye a jihar Bornon Nigeria.
Mazauna kauyen Gumsiri da ke karamar hukumar Damboa,
sun shaida wa BBC cewar an kai harin ne a ranar Lahadi
kafin mayakan su tattara mata da kananan yara su wuce da
su.
Sai dai wani dan kauyen Gumsiri wanda ya gudu zuwa
Maiduguri, ya ce mutane fiye da 200 aka sace bayan sun bi
gida-gida sun kirga yawan mutanen da ba a gani ba.
Kawo yanzu babu wata hanyar tantance adadin wadanda
lamarin ya rutsa da su, saboda akwai yiwuwar wasu daga
cikin mutanen sun fantsama cikin daji ne domin neman
tsira.
Wani jami'in karamar hukuma ya ce "Mutanen sun tattara
mata da kananan yara sannan suka tafi da su a cikin
manyan motoci kafin su bankawa kauyen wuta."
Labarin harin na zuwa ne bayan kwanaki hudu saboda babu
hanyoyin sadarwa a kauyukan jihar Borno.
source bbchausa
Title :
'Yan Boko Haram sun sace mutane 200 a
Borno
Description : Mayakan Boko Haram sun sace mata da kananan yara kusan 200 sannan kuma suka kashe mutane fiye da 30 a wani kauye a jihar Bornon Nigeria. ...
Rating :
5